Wannan auren zai yi zafi: Amarya tayi banza da Angonta wajen Walimar Aure

Wannan auren zai yi zafi: Amarya tayi banza da Angonta wajen Walimar Aure

  • An yi gajeriyar Dirama a wani walimar daurin aure a Ughelli, jihar Delta yayinda aka shaida abinda ke faruwa tsakanin Ango da Amarya
  • Don wasu dalilai, da alamun Amaryar na fushi da Angonta saboda yadda tayi banza da shi yayinda yake kokarin magana da ita
  • Mutane a kafafen sada ra'ayi da sada zumunta sun bayyana ra'ayoyinsu kan wannan abu

Ughelli, jihar Delta - Gajeriyar Dirama ta auku a bikin daurin aure kuma mutane da dama sun tofa albarkatun bakinsu a kafafen ra'ayi da sada zumunta.

Abinda ya faru shine Amaryar ta yi burus da Angonta, yayinda yake kokarin yi mata magana.

Shafin Instablog9ja ta daura bidiyon abinda ya auku a dandalin Instagram.

Wannan auren zai yi zafi: Amarya tayi banza da Angonta wajen Walimar Aure
Wannan auren zai yi zafi: Amarya tayi banza da Angonta wajen Walimar Aure Hoto:Instablog9ja
Asali: Instagram

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Adadin mutanen da suka mutu sakamakon rushewar gini a Legas ya karu zuwa 36

A bidiyon na yan sakonni, Amaryar tana gudun magana da mijin yayinda yake kokarin hira da ita.

Wannan abu ya auku ne a garin Ughelli, jihar Delta.

Kalli bidiyon:

Mutane sun tofa albarkatun bakinsu

Sagir Saleh Haruna yace:

Ta wani tura Baki gaba, Ina ruwan gumba

Haruna Jibrin yace:

Karyadamu dadaren yazo zatamanta

Najeeb Harande yace:

Lol, se yayi ahankali dan mata ba kanwar lasa bane wasu lokutta

Zira V Kwada yace:

Tun ba a je ko ina ba.

Abubakar Audu Mustapha yace:

Kuma gata mummunaba

Idris Musa Nyabo yace:

Lallai wannan ya hau motar Abbatoir

Asali: Legit.ng

Online view pixel