Bidiyon hamshakan yan kasuwa sanye da kayan harami cikin jirgi ya bayyana

Bidiyon hamshakan yan kasuwa sanye da kayan harami cikin jirgi ya bayyana

  • Wani bidiyon hamshakan attajiran Najeriya cikin jirgi a kasar Saudiyya ya ja ra'ayin mutane a kafafen sada zumunta
  • Wasu sun siffanta wannan tafiya matsayin mafi tsada saboda irin masu arzikin dake cikin jirgin
  • Yayinda mutum mafi arziki a nahiyar Afrika, Aliko Dangote ke danna wayarsa, sauran na tattaunawa

Attajirin nahiyar Afrika, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cikin bidiyo tare da attajirai irinsu cikin jirgin sama.

Wisdom Blogg ce ta daura wannan bidiyo a shafin Instagram.

A cikin faifan bidiyon an ga Aliko Dangote tare da wasu cikin jirgin sanya da kayan Ibadah na Umrah da suka gudanar a Makkah.

Daga cikin wadanda ke cikin jirgin akwai shugaban kamfanin BUA, Alhaji Abdul Samad Isyaka Rabiu, da kuma Shugaban kamfanin jirgin MaxAir, Alhaji Dahiru Mangal, dss.

Yan Najeriya da dama sun bayyana cewa wannan haduwa ake nufi da Naira na gugan Naira.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari Ya dawo daga Kasar Saudiyya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bidiyon hamshakan yan kasuwa
Bidiyon hamshakan yan kasuwa sanye da kayan harami cikin jirgi ya bayyana Hotuna: @wisdomblogg
Asali: Instagram

Dangote, AbdulSamad, Mangal, Shugaba Buhari sun gudanar da aikin Umrah

Manyan attajirai da yan kasuwa sun garzaya Makkah domin gudanar da aikin Umrah bayan taron zuba jarin da suka halarta tare da shugaba Muhammadu Buhari a Riyadh.

Hakazalika Shugaba Buhari tare da hadimansa sun shiga Ibadar da yammacin Laraba, 27 ga watan Oktoba, 2021.

An ga hotunan manyan attajiran tare.

Shugaba Buhari ya dawo gida

Tuni dai Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya dira a birnin tarayya Abuja da yammacin Juma'a, 29 ga Oktoba, bayan tafiyar kwana biyar da yayi Kasar Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ta ruwaito cewa Shugaba Buhari da mukarrabansa sun tashi daga filin jirgin Sarki AbdulAzizi dake Jiddah misalin karfe 15:45.

A kwanaki biyar da yayi a Saudiyya, Buhari ya ziyarci Riyadh, Makkah da Madina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel