Shugaban sojoji ya ba da umarnin a saki sojar da ta fada soyayya da kopa a sansanin NYSC

Shugaban sojoji ya ba da umarnin a saki sojar da ta fada soyayya da kopa a sansanin NYSC

  • Babban Hafsan Sojojin Najeriya (COAS), Laftanar-Janar. Faruk Yahaya ya bada umarnin cewa a saki Pte. Hannah Sofiat A. wata Soja mace da ake tsare da ita saboda fadawa soyayya
  • Rundunar soja ta tsare Sofiat ne saboda ta karya doka da ka’ida ta hanyar kulla wata alakar soyayya da wani dan bautar kasa a Kwara
  • An gafartawa sojan kuma an sake ta don shiga sake ganawa da danginta da abokanta don yin bikin Kirsimeti

Abuja - An saki Pte. Hannah Sofiat A, wata soja a Najeriya da ta amince da bukatar soyayyar wani dan bautar kasa a sansanin NYSC da ke Yikpata ta jihar Kwara.

Jaridar The Nation ta bayyana cewa babban hafsan sojin kasa (COAS), Lt.-Gen. Faruk Yahaya ya bada umarnin a gaggauta sakin Sofiat bayan an tsare ta na 'yan kwanaki.

Kara karanta wannan

Mutum 7 sun rasa rayukansu a mumunan hadarin da ya auku ranar Kirismeti

Soja da Kopa sun fada soyayya
Shugaban sojoji ya ba da umarnin a saki sojar da ta fada soyayya da kopa a sansanin NYSC | thecable.ng
Asali: UGC

Ku tuna cewa wannar sojan ta shiga matsala bayan da wani faifan bidiyo da ke nuna wani dan bautar kasa na neman aurenta ya yadu a shafukan sada zumunta.

Wata majiya a hedikwatar rundunar soji a ranar Asabar, 25 ga watan Disamba, ta bayyana cewa shugaban rundunar sojin Najeriya ya amince da matakin sakin sojar saboda Kirsimeti, in ji jaridar The Guardian.

Wannan ya faru ne daidai lokacin da ake son samun kwararrun sojojin Najeriya da ke shirye don cimma ayyukan da aka sa a gaba a cikin hadin gwiwar tsaron Najeriya.

Da take karin bayani, majiyar ta kara da cewa, an gargadi Sofiat da kuma tsawatar mata kan saba ka’idar da ta yi na fadawa soyayya yayin da take bakin aiki.

An gafarta mata kuma an sake ta a daidai lokacin da ta shiga danginta da abokanta don yin shagalin bikin Kirsimeti.

Kara karanta wannan

Sanata Shehu Sani ya gwangwanje jami'an kan hanya da kyautukan kirsimeti a Kaduna

Wata soja ta gamu da fushin gidan soja yayin da ta amince za ta auri dan bautar kasa

A tun farko, Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da tsare wata Soja da ta amince da bukatar auren wani dan bautar kasa a sansanin NYSC da ke Kwara.

Bidiyon masoyan da ke yawo an ga lokacin da suke abubuwan karbar soyayyar juna, lamarin da ya haifar da cin kalamai iri-iri a dandalin sada zumunta.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar soji Onyema Nwachukwu ya aika wa TheCable Lifestyle a ranar Lahadi, ya ce sojar dai ta karya wasu ka’idojin gidan sojoji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel