Mutum 7 sun rasa rayukansu a mumunan hadarin da ya auku ranar Kirismeti

Mutum 7 sun rasa rayukansu a mumunan hadarin da ya auku ranar Kirismeti

  • Wani mumunan hadarin mota ya auku ranar Asabar, 25 ga Disamba, a babban titin Sagamu-Ore dake jihar Ogun
  • Rahotannin sun nuna cewa an yi rashin rayuka akalla bakwai yayinda fasinjoji da dama suka jigata
  • Sakta Kwamanda na hukumar FRSC ya tabbatar da aukuwar hadarin ta bakin jami'ar wayar da kai, Florence Okpe

Sagamu, Ogun - Akalla rayuka bakwai sun salwanta yayinda wasu suka jigata a wani mumunan hadarin motan da ya auku ranar Kirismeti a jihar Ogun.

Daily Trust ta ruwaito cewa wata mota kirar Mercedes Benz MarcoPolo ta yi hadari ne a titin Sagamu-Benin-Ore da cikin daren Asabar misalin karfe 12:00.

A cewar rahoton, motar ta tashi daga Ojuelegba da Legas kuma ta nufi kudu maso gabas.

Jami'ar wayar da kan jama'a a hukumar kiyaye hadura FRSC, Florence Okpe, ta tabbatar da aukuwar lamarin a jawabin da ta saki.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sheke mutum 7 a kusa da matsayar sojoji, sun sace wasu a Katsina da Kaduna

Okpe tace mutum 63 ke cikin motar; maza 40, mata 15 da yara takwas.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutum 7 sun rasa rayukansu a mumunan hadarin da ya auku ranar Kirismeti
Mutum 7 sun rasa rayukansu a mumunan hadarin da ya auku ranar Kirismeti
Asali: UGC

Me ya haddasa hadarin?

Jami'ar ta bayyana cewa motar ta kwacewa direban ne yayinda yake kokarin wuce wata motar ba bisa tsari ba.

Okpe tace:

"An duba lafiyar wadanda suka jikkata yayinda aka ajiye gawawwakin wadanda suka mutu a dakin ajiyan gawan asbitin jihar dake Ijebu Ode."
"An tuntubi ofishin yan sandan Odogbolu kuma an mika musu motar da tayi hadari don dauketa daga hanya."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel