Zaben Anambra 2021: Dalilai 4 da za su iya sa Charles Soludo ya lashe zabe

Zaben Anambra 2021: Dalilai 4 da za su iya sa Charles Soludo ya lashe zabe

Duk da akwai 'yan takara 18 tare da jerin jam'iyyun siyasa da suka fito gaba-gadi domin neman kujerar gwamnan jihar Anambra a zaben da za a yi ranar 6 ga watan Nuwamba, akwai 'yan takarar da babu shakka za a fafata da su.

Daga cikin 'yan takarar akwai Fafesa Charles Chukwuma Soludo, wanda shi ne dan takarar jam'iyya mai mulki a jihar ta All Progressives Grand Alliance (APGA).

Zaben Anambra 2021: Dalilai 4 da za su iya sa Charles Soludo ya lashe zabe
Zaben Anambra 2021: Dalilai 4 da za su iya sa Charles Soludo ya lashe zabe. Hoto daga Charles Chukwuma Soludo
Asali: Facebook

Ga wasu manyan dalilai hudu da za su iya sa tsohon gwamnan babban bankin Najeriyan ya samu nasarar lashe zaben.

1. Karfin ikon masu madafun iko

Daya daga cikin abubuwan da za su iya saka Soludo ya yi nasarar shi ne, ikon da suke da shi na cewa jam'iyyarsu ke mulki.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun ceto malaman UNIAbuja da aka sace, an kama 'yan bindiga

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A Najeriya da kasashe masu yawa da ke mulkin damokaradiyya a duniya, matukar wanda ke kan madafun iko ko kuma dan takarar jam'iyya mai mulki, ya na da wata dama fiye da sauran 'yan takara.

A sama da shekaru 15, daga Peter Obi zuwa Willie Obiano, APGA ta kasance jam'iyyar da ke mulkin Anambra. Ita kadai ce jihar da jam'iyyar ke mulki a Najeriya.

Duk da zama dan takarar jam'iyya mai mulki bashi da tabbacin cin zabe, ta yuwu gwamnan babban bankin ya lashe zaben.

2. Bayanin martabar Soludo

Daga cikin 'yan takarar kujerar gwamnan jihar Anambra, martabar Soludo ta zama ta daban. Baya ga shugabantar babban bankin Najeriya, Soludo ya na da wata gogewa a zaman da yayi mai bada shawara kan tattalin arziki ga shugabannin kasa: Olusegun Obasanjo da Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Matashi dan shekara 36 daga arewa yana neman 'kujera ta daya' a APC

A matsayinsa na Farfesan tattalin arziki, Soludo ya yi aiki a bangarorin kudi daban-daban na duniya.

3. Sanayyarsa da jama'ar Anambra da kuma siyasar yankin

A matsayinsa na tsohon dan takara kujerar gwamna karkashin jam'iyyar PDP a 2010, Soludo ya na fahimtar siyasar Anambra kuma sanin shi da 'yan jihar suka yi abun dubawa ne.

4. Kokarin da yayi a lokacin fafatawa da sauran 'yan takara

A ranar Litinin, 1 ga watan Nuwamba, Soludo da 'yan takarar APC da na PDP sun fafata a wata muhawara da gidan talabijin da Arise News ta shirya.

Babu shakka Soludo ya zama zakaran gwajin dafi wanda kuma ya tafi da zukatan masu kada kuri'a da yawa a Anambra.

Zaben Anambra: IGP ya tura manyan 'yan sanda sama da 100 kan barazanar IPOB

A wani labari na daban, Kafin zuwan zaben gwamnoni na 6 ga watan Nuwamba a jihar Anambra, sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Usman Baba, ya aike a kalla manyan jami'an 'yan sanda dari domin samar da tsaro isasshe a jihar.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun bindige jami’an yan sanda 4 a jahar Anambra

Wannan na zuwa ne ana tsaka da tsoro tare da fargabar barazanar da 'yan awaren IPOB ke yi na hargitsa zaben, Daily Trust ta wallafa.

Daga cikin jami'an 'yan sanda da aka tura jihar Anambra akwai mataimakan sifeta janar na 'yan sanda 4, kwamishinonin 'yan sanda 14, mataimakan kwamishinonin 'yan sanda 31 da kuma wasu manyan jami'ai 48.

Asali: Legit.ng

Online view pixel