Zaben Anambra: Ƙuri'ar jin ra'ayi da wani kamfanin Amurka yayi ya nuna jam'iyyar da za ta lashe zaɓen gwamna

Zaben Anambra: Ƙuri'ar jin ra'ayi da wani kamfanin Amurka yayi ya nuna jam'iyyar da za ta lashe zaɓen gwamna

  • Wani kamfanin shawarari na Hallmark International da ke Amurka ya yi kiyasi akan cewa Sanata Andy Uba ne zai lashe zaben gwamnoni da za ayi na jihar Anambra ranar 6 ga watan Nuwamba
  • Kamfanin na bincike da bayar da shawarwari akan siyasa ya yi nuni da cewa Uba zai ci nasarar da yuwuwa tazarar sa da Soludo ta zama tsakanin kaso 3 zuwa 4%
  • Mataimakin shugaban kamfanin na nahiyar Afirka da gabas ta tsakiya, Hayes Rodney ya ce hankalin kamfanin ya karkata akan zaben ne ba goyon bayan wata jam’iyya su ke yi ba

Wani kamfani na shawarwari akan harkokin siyasa da gudanar da bincike na kasa da kasa da ke Amurka ya ce akwai yiwuwar Andy Uba na jam’iyyar APC ya lashe zaben da za a yi na gwamnoni a Anambra na ranar 6 ga watan Nuwamba.

Read also

Zaben Anambra: Bayani a kan ‘Dan takarar APC wanda ya taba yin Gwamna na kwana 17

Bisa ruwayar The Punch, kamfanin na bincike ya gudanar da kuri’ar jin ra’ayi wacce gidauniyar ‘Power to the People’ ta aiwatar akan ‘yan takara 6 kuma manuniya ta nuna wanda zai iya ci nasara.

Anambra 2021: Ƙuri'ar jin ra'ayi da wani kamfanin Amurka ya yi ya bayyana jam'iyyar da za ta lashe zaɓe
Kuri'ar jin ra'ayi da wani kamfanin Amurka ya yi ya bayyana jam'iyyar da za ta lashe zaɓen gwamnan Anambra: @RealAndyUba
Source: Facebook

A cikin ‘yan takarar akwai Godwin Maduka na jam’iyyar Accord, Charles Soludo na APGA, Valentine Ozigbo na PDP, Obiora Okonkwo na ZLP da kuma Sanata Andy Uba na jam’iyyar APC.

Rahotonni sun fi mayar da hankali akan ‘yan takarar gwamnan guda biyu, Soludo da Uba, inda ya kula da cewa dan takarar APC zai iya cin nasara da tazarar 3 zuwa 4% a zaben mai zafi da za a gudanar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamfanin da ke Ingila ya kafa wata kungiya mai zaman kan ta da za ta samar da dorewar demokradiyya a Afirka da duniya don samar da kuri’ar jin ra’ayi, kamar yadda Leadership ta bayyana.

Read also

Zaben Shugabanni: APC tana ta tangal-tangal, ana fama da rigingimu a Jihohi 13

Gidauniyar, a wata takarda da mataimakin shugaban ta na Afirka da gabas ta tsakiya, Hayes Rodney ya ce, ta mayar da hankali akan zaben ne ba wata jam’iyya ba.

Yanzu-yanzu: Ƙungiyar IPOB ta saduda, ta soke dokar zaman gida na dole, ta ce a fita a yi zaɓe a Anambra

A wani rahoton, kun ji cewa haramtaciyyar kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) ta soke dokar da ta saka na zama gida na dole a yankin kudu mazo gabas, rahoton The Cable.

Haramtaciyyar kungiyar ta yi barazanar hana harkoki baki daya a yankin kudu maso gabas din daga ranar 5 ga watan Nuwamba.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa hakan na zuwa ne bayan da gwamnatin tarayya ta tura jami'an tsaro da dama jihar ta Anambra yayin da ake shirin yin zaben a ranar Asabar.

Source: Legit.ng

Online view pixel