Zaben Shugabanni: APC tana ta tangal-tangal, ana fama da rigingimu a Jihohi 13

Zaben Shugabanni: APC tana ta tangal-tangal, ana fama da rigingimu a Jihohi 13

  • Har yanzu jam’iyyar APC mai mulki ta gagara sa ranar da za ta gudanar da zaben shugabanni na kasa
  • Tun tuni ake ta sa rana, amma ana kara lokacin, kuma babu alamun za ayi zaben cikin kwanan nan
  • John Akpanudoedehe yace ba za a iya zabe ba, sai an yi wa ‘ya ‘yan jam’iyya rajista a duk jihohi 36

Abuja - Jam’iyyar APC ba ta ga ma cin matsaya a game da ranar da za ta shirya zaben shugabanni na kasa ba. Jaridar Punch ce ta fitar da wannan rahoto.

Tun 2020 ya kamata ayi zaben, amma aka yi ta dagawa. Da farko an tsaida watan Yunin 2021, sai kuma aka sake karawa su Mai Mala Buni watanni shida.

Daga cikin abubuwan da suka jawo aka gaza tsaida lokacin babban gangami na kasa shi ne ba ayi wa ‘ya ‘yan jam’iyya rajista a jihohin Zamfara da Anambra ba.

Read also

A dage zaben gwamnan Anambra domin kare rayuka – Babban fasto ga FG

Sannan jam’iyyar APC mai mulki tana fama da matsaloli iri-iri a sakamakon zaben shugabanni da aka gudanar a jihohi, kananan hukumomi da mazabu.

Akwai jihohi akalla 13 da rigingimu suka barke bayan an shirya zaben shugabanni na jam’iyya. ‘Yan taware sun sha alwashi ba za su janye kara a kotu ba.

Shugabannin APC
Jigogin APC a Aso Villa Hoto: thewhistler.ng
Source: UGC

Majiya daga jam’iyyar ta shaidawa Punch cewa APC ba za ta gudanar da zabe ana faman rikici ba.

“Akwai abubuwa da dama da ya kamata mu shawo kansu. Sai mun yi wannan sannan za mu sa ranar da za ayi zabe na kasa.” Inji wani ‘dan jam’iyya.

Idan muka yi zabe, za a iya zuwa kotu - Akpanudoedehe.

Sakataren APC na rikon kwarya na kasa, Sanata John Akpanudoedehe ya shaidawa manema labarai cewa sai an kakkabe wasu kura kafin a iya yin zabe.

Read also

Shehu Sani: Kashe Sheƙau da Al-Barnawi ba zai kawo ƙarshen ta'addanci ba

“Ka duba dokar APC, idan muka yi zabe, mu ka bar ko da jiha daya ne, mutum yana iya zuwa kotu, ya kai korafin an yi babu shi.” – Akpanudoedehe.

Watakila sai bayan zaben Anambra za a sa ranar da za a zabi shugabanni. Akpanudoedehe ya kuma tabbatar da cewa ba za suyi wani zabe na shiyyoyi ba.

Tambuwal Volunteers tace sai Tambuwal

A jiya aka ji kungiyar wasu matasan Arewa mai suna Tambuwal Volunteers tana cewa ana fama da rashin tsaro, yunwa, talauci da rabuwar kai a Najeriya.

A game da zaben 2023, Kungiyar ‘Yan Arewan ba ta goyon bayan karba-karba, tace tana goyon bayan Aminu Tambuwal ya yi itakara domin ya gyara kasa.

Source: Legit.ng

Online view pixel