Rundunar yan sanda ta tabbatar da sace tsohon shugaban NPA a Kano

Rundunar yan sanda ta tabbatar da sace tsohon shugaban NPA a Kano

  • Hukumar yan sandan Kano ta tabbatar da sace tsohon shugaban hukumar tashoshin jiragen ruwa na Najeriya, Bashir Abdullahi
  • Rundunar ta ce tuni aka tura wata tawagar tsaro ta Operation Puff Adder domin su ceto wanda abun ya rutsa da shi tare da kama masu laifin
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar, DSP Haruna Abdullahi ya tabbatar da hakan

Jihar Kano - Rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da sace tsohon janar manajan hukumar tashoshin jiragen ruwa na Najeriya, Bashir Abdullahi.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar, DSP Haruna Abdullahi ya saki ga manema labarai a ranar Alhamis, 4 ga watan Nuwamba, rahoton Punch.

Rundunar yan sanda ta tabbatar da sace tsohon shugaban NPA a Kano
Rundunar yan sanda ta tabbatar da sace tsohon shugaban NPA a Kano Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A cewar Abdullahi:

"An tura wata tawagar tsaro ta Operation Puff Adder domin su ceto wanda abun ya rutsa da shi tare da kama masu laifin."

Kara karanta wannan

Miyagun yan bindiga sun bi tsakar dare sun yi awon gaba da mata zalla a Neja

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

"A ranar 03/11/2021 da misalin karfe 1630, mun samu wani rahoton cewa, wasu yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun sace wani Bashir Abdullahi mai shekaru 65 na kauyen Sitti, karamar hukumar Samaila, jihar Kano, a gonarsa da ke dajin Barasa, kauyen Gomo, karamar hukumar Sumaila, jihar Kano, wani iyaka da jihar Bauchi.
"Da samun rahoton, kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya tashi sannan ya umurci tawagar tsaro na Operation Puff Adder da su ceto mutumin sannan su kama masu laifin."

Ya ce tuni tawagar suka shiga aiki inda ya kara da cewa binciken farko ya nuna cewa wanda abun ya cika da shi ya koma gonar da zama tun makonni biyu da suka gabata.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun bindige jami’an yan sanda 4 a jahar Anambra

AIT News ta rahoto cewa an bindiga sun sace Abdullahi ne daga gonarsa da ke karamar hukumar Sumaila na jihar Kano a ranar Laraba, 3 ga watan Nuwamba.

Zuwa yanzu dai babu wani cikakken bayani a kan sace tsohon shugabab na NPA.

A wani labari na daban, mun ji cewa yan kwanaki kafin zaben gwamna a jihar Anambra, wasu yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kashe jami'an yan sanda hudu a garin Oraifite da ke karamar hukumar Ekwusigo na jihar.

Lamarin ya afku ne a safiyar ranar Alhamis, 4 ga watan Nuwamba, bayan maharan sun bude wuta a kan jami'an tsaron, jaridar PM News ta rahoto.

Harin ya kara haifar da fargaba a tsakanin jami'an tsaro da ke gudanar da aikin zabe da kuma mazauna jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel