Ba mu da hannu a kama Nnamdi Kanu, gwamnatin kasar Kenya ta fadawa kotu

Ba mu da hannu a kama Nnamdi Kanu, gwamnatin kasar Kenya ta fadawa kotu

  • A karo na biyu, gwamnatin kasar Kenya ta nisanta kan ta daga kama da kuma rike shugaban kungiyar rajin kafa kasar Biafra ta IPOB, Mazi Nnamdi Kanu
  • Gwamnatin ta bayyana hakan a kotu yayin da dan’uwan Kanu, Kingsley Kanunta Kanu ya kai karar a maimakon shugaban kungiyar IPOB din
  • An samu wannan rahoton ne ta wata takarda wacce dan’uwan kanu ta hannun lauyan Kanu na musamman, Aloy Ejimakor ya bai wa manema labarai bayan shari’ar a Kenya ranar 2 ga watan Nuwamba

Kasar Kenya - Gwamnatin kasar Kenya ta kara nisanta kan ta daga kama shugaban haramtaciyyar kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra ta IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, rahoton Vanguard.

Gwamnatin yayin kare kan ta a kotun da dan uwan Kanu, Kingsley Kanunta Kanu ya shigar da kara a maimakon shugaban IPOB din, gwamnatin kasar Kenya ta ce ba da izinin hukuma gwamnati ta kama Kanu ba.

Kara karanta wannan

An yi wata 10 babu wuta a Borno, Manyan Arewa sun yi kaca-kaca da Gwamnatin Buhari

Ba mu da hannu a kama Nnamdi Kanu, gwamnatin kasar Kenya ta fadawa kotu
Ba mu da hannu a kama Nnamdi Kanu, gwamnatin kasar Kenya ta fadawa kotu. Hoto: Ugonna Chukwudi

Takardar da lauyan Kanu na musamman, Aloy Ejimakor ya gabatar wa Vanguard a maimakon dan’uwan Kanu ta nuna bayan zaman kotun ranar 2 ga watan Nuwamba ta nuna hakan.

Kenya ba ta da hannu a kamen Kanu

Takardar ta nuna yadda gwamnatin Kenya ta ce babu wata takarda a wani ofishin ‘yan sanda ko kuma wata hukuma da ta bayar da umarnin kama Kanu a Kenya.

A wani yanki na takardar kanin Kanu ya ce:

“A ranar 2 ga watan Nuwamban 2021, gwamnatin Kenya ta kare kan ta daga karar da na maka a maimakon dan’uwa na Mazi Nnamdi Kanu.
“Idan ba a manta ba bayan kama dan’uwa na a Yunin wannan shekarar, gwamnatin Kenya ta fitar da takarda inda ya nuna cewa ba ta da hannu a wannan aika-aikan."

Kara karanta wannan

Nnamdi Kanu ya fi zaben Anambra muhimmanci, ku sake shi don a samu zaman lafiya, Doyin Okupe

Ya kara da bayyana yadda gwamnatin jihar ta bayyana cewa babu wata takarda wacce take nuna da umarnin hukuma don kama Kanu.

Ya kara da cewa hakan ya na nuna cewa ba bisa ka’ida aka dauko Kanu daga Kenya zuwa Najeriya ba kamar yadda gwamnatin Najeriya ta nuna.

Za a sake wani zaman kotu a ranar 7 ga watan Disamban 2021 inda za a kara jin ta bakin bangarorin.

Yanzu-yanzu: Ƙungiyar IPOB ta saduda, ta soke dokar zaman gida na dole, ta ce a fita a yi zaɓe a Anambra

A wani rahoton, kun ji cewa haramtaciyyar kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) ta soke dokar da ta saka na zama gida na dole a yankin kudu mazo gabas, rahoton The Cable.

Haramtaciyyar kungiyar ta yi barazanar hana harkoki baki daya a yankin kudu maso gabas din daga ranar 5 ga watan Nuwamba.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa hakan na zuwa ne bayan da gwamnatin tarayya ta tura jami'an tsaro da dama jihar ta Anambra yayin da ake shirin yin zaben a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Harin da aka kai gidan Odili ya fi kama da yunkurin halaka wa ko nakasa ta, Kotun koli

Asali: Legit.ng

Online view pixel