Harin da aka kai gidan Odili ya fi kama da yunkurin halaka wa ko nakasa ta, Kotun koli

Harin da aka kai gidan Odili ya fi kama da yunkurin halaka wa ko nakasa ta, Kotun koli

  • Kotun kolin Najeriya ta nuna damuwar ta tare da fushi kan harin da jami'an tsaro suka kai gidan Mary Odili
  • Kamar yadda kotun ta bayyana, harin ya fi kama da yunkurin halaka mai shari'ar ko kuma nakasa ta
  • A cewar takardar da kotun ta fitar ranar Talata, wannan ya fi kama da kauyanci tare da mayar da kai baya

FCT, Abuja - Hukumar kotun koli a ranar Talata ta magantu kan harin da aka kai gida mai shari'a Mary Odili a ranar Juma'a da ta gabata.

A wata takardar da daraktan yada labarai, Festus Akande, na kotun kolin ya fitar, ya ce kutsen ya fi kama da yunkurin kashe alkalin ko kuma nakasa ta.

Premium Times ta ruwaito cewa, takardar ta ce an kai hari ne da sunan an je bincike wanda kuma takardar izinin binciken ba ta da tushe kuma cike ta ke da kauyanci tare da abun kunya.

Kara karanta wannan

Dalla-dalla: Dalilai 2 da suka sa EFCC ta yi ram da biloniya Obi Cubana

Harin da aka kai gidan Odili ya fi kama da yunkurin halaka wa ko nakasa ta, Kotun koli
Harin da aka kai gidan Odili ya fi kama da yunkurin halaka wa ko nakasa ta, Kotun koli. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC
"Mun samu labarin wani irin hari da aka kai gidan daya daga cikin manyan alkalan kotun koli, Mai shari'a Mary Peter Odili a ranar Juma'a, 29 ga watan Oktoba ta wata hanya mara kyau.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wasu ne da ake zargin jami'an tsaro ne dauke da makamai wadanda ke wakiltar wasu cibiyoyin gwamnati. Da alama sun je kashe ta ko nakasa ta ne inda suka boye da sunan zuwa bincike gidan.
"Mun yi matukar takaici kuma an mayar da mu baya ta hanyar wannan abun kauyancin da na kunya wanda aka yi wa jami'ar shari'a wacce ta kwashe shekaru masu muhimmanci na rayuwar ta ta na bauta wa kasar ta," takardar tace.

A yayin kushe harin, kotun kolin ta barranta kanta da irin harin wanda hukumar tsaro ta farin kaya ke kai wa gidajen wasu manyan alkalai da suka hada da alkalai biyu na kotun koli a Abuja da wasu sassan kasar nan a 2016, Premium Times ta wallafa.

Kara karanta wannan

Kaduna: Duk da datse layikan sadarwa, 'yan bindiga sun sace mutum 9, sun bukaci N50m

Jami'an tsaro sun dira gidan alkalin kotun koli a Abuja

A wani labari na daban, Jami'an tsaro a ranar Juma'a sun dira gidan Mary Odili, alkali a kotun koli da ke Abuja.

Alkalin kotun kolin mata ce ga Peter Odili, tsohon gwamnan jihar Ribas wanda a halin yanzu ya ke cikin wadanda hukumar yaki da rashawa ta kasa, EFCC suka sanya wa ido.

Kamar yadda TheCable ta wallafa, Har yanzu dai babu cikakken bayani kan abinda ke faruwa a gidan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel