Yadda wata yar bautar kasa NYSC ta mutu a Legas bayan ta guje wa matsalar tsaro a Borno

Yadda wata yar bautar kasa NYSC ta mutu a Legas bayan ta guje wa matsalar tsaro a Borno

  • Wata yar bautar ƙasa NYSC, Zaynab Sanni Oyindamola, ta rasa rayuwarta a dogon ginin da ya kife a Legas
  • Mahaifiyar Zaynab ce ta samar mata da canjin wuri, bayan da farko an tura ta jihar Borno, inda ta ɗauki horo na tsawon mako uku
  • Wani daga cikin yan uwanta yace ba su so zuwan ta jihar Borno ba, amma da sun san haka zata faru da sun barta a can

Lagos - Dailytrust tace mahaifiyar Zaynab Sanni Oyindamola, wata mambar NYSC ta samar wa ɗiyarta canjin wurin aiki daga jihar Borno saboda rashin tsaro.

Hakanan kuma mahaifiyar tana son ɗiyarta ta yi aiki a wuri mai tsaro kuma wanda bata sani ba, amma ashe hakan wata ƙaddara ce take kiranta.

Read also

Aƙalla mutum 7 suka mutu yayin da miyagun yan bindiga suka kai harin farko yankin wannan jihar

Zaynab Oyindamola, tana ɗaya daga cikin waɗan da kifewar dogon gini mai hawa 21 ya rutsa da su a Legas, kuma tana cikin mamata.

Zainab Sanni
Yadda wata yar bautar kasa NYSC ta mutu a Legas bayan ta guje wa matsalar tsaro a Borno Hoto: dailytrust.com
Source: UGC

Rahoto ya tabbatar da cewa Zaynab tana ɗaya daga cikin yan bautar ƙasa NYSC mutum 6 da aka tura su yi aiki a kamfanin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shin NYSC ta san da lamarin?

Wata majiya daga cikin NYSC ta shaida wa manema labarai cewa Zaynab Oyindamola, kaɗai ce suka tabbatar da mutuwar ta zuwa yanzun.

Majiyar tace:

"Oyin kamar yadda ake kiranta a taƙaice, tana daya daga cikin mambobin NYSC na rukunin B 2021, waɗan da aka tura jihar Borno, amma ta samu canji zuwa Legas bayan kammala ɗaukar horo na mako uku."

Yadda mutane ke jimamin mutuwarta

Bayan tabbatar da mutuwarta, kawayenta da abokanan arziki suka fara jimami a kafafen sada zumunta.

Read also

Tashin Hankali: Babban bututun iskar Gas ya fara kwarara cikin Jama'a a jihar Legas

Daya daga cikinsu, Agboola Yusuf Olatunji, wanda ya saka hotonta yace:

"Tana daga cikin waɗannan rushewar gini ya rutsa da su, kuma mun rasa ta. Allah ya jikanki da rahama Sanni Zainab, muna kaunarki amma wanda ya halicce mu ya fi sonki."

Yaushe ta fara zuwa aikin kamfanin?

Ɗaya daga cikin iyalanta, ya bayyana cewa Zainab Oyindamola, ta fara zuwa aiki da kamfanin ne mako uku da suka gabata.

"Ta jima tana zuwa kamfanin, bamu san dalilin tura ta nan ba, amma da farko jihar Borno aka tura ta, mahaifiyarta tasa aka dawo da ita nan."
"Sai da muka ce karta je Borno, amma ta tafi ɗaukar horo na tsawon mako uku ta dawo lafiya. Da mun san haka zata faru da mun barta a can ta yi aikinta."

A wani labarin kuma yayin da labarin mutuwar kasurgumin ɗan bindiga Dogo Gide ta karaɗe kafafen watsa labarai, mun gudanar da bincike kan sahihancin labarin.

Read also

Ko ta wane hali zan nemi kujerar shugaban ƙasa a 2023, Tsohon shugaban majalisar dattijai

A cewar labaran da ake yaɗawa mataimakinsa ne ya bindige shi har Lahira, to amma shin dagaske haka ta faru?

Bincike daga masana da kuma masu rubutu a kan al'amuran yan bindiga a Arewa ta yamma ya tabbatar da abinda ke faruwa.

Source: Legit.ng

Online view pixel