Mun san ranar da za'a daina sata da garkuwa da mutane a Najeriya, Hukumar leken asiri

Mun san ranar da za'a daina sata da garkuwa da mutane a Najeriya, Hukumar leken asiri

  • Babban jami'in gwamnatin tarayya ya bayyana cewa sun yi hasashen ranar da garkuwa da mutane zai zama tarihi a Najeriya
  • Shugaban na hukumar NFIU yace sun samar da wani shiri na musamman da ke taimaka musu wajen wannan hasashe
  • A kan Boko Haram, yace mafi yawancin mayakan sun mika wuya kuma an karya lagonsu a Najeriya

Abuja - Shugaban hukumar leken asirin kudade watau NIFU, Mr Modibbo Tukur, ya bayyana cewa nan da watan Afrilun 2022, za'a daina sata da garkuwa da mutane a Najeriya.

Hukumar NFIU wata sashe ce na Babban bankin Najeriy CBM dake bibiyan masu daukar nauyin yan ta'adda, da yaki da barayi masu kai kudaden Najeriya waje.

Moddibo ya bayyana hakan ne a taron waksho da aka shirya kan yaki da safarar kudade da kuma daukar nauyin ta'addancin ranar Talata a Abuja, rahoton DailyTrust.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta karbi bashin N8.29 trillion cikin kudin yan fansho dake ajiye a banki

A cewarsa:

"Ranar karshen yan bindiga da masu garkuwa da mutane tsakanin Maris da Afrilun 2022 ne."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban hukumar leken asiri
Mun san ranar da za'a daina sata da garkuwa da mutane a Najeriya, Shugaban hukumar leken asiri Hoto: NFIU
Asali: Twitter

Moddibo yace sun yi wannan hasashe ne bisa binciken da ma'aikatar ta gudanar, kuma irin wannan hasashe akayi na ganin karshen yan ta'addan Boko Haram, riwayar Vanguard.

Yace ranar da 15 ga Satumba 2021 aka yi hasashe zai kasance karshe Boko Haram a Najeriya kuma an cimma wannan.

A cewarsa, an cimma wannan nasara ne sakamakon toshe hanyoyin da yan ta'addan Boko Haram ke samun kudi kuma yanzu yankin Arewa maso gabas ta fi zaman lafiya da Arewa maso yamma dake fama da matsalar garkuwa da mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel