IGP Usman Baba: Babu makawa za a yi zaben gwamna a jihar Anambra

IGP Usman Baba: Babu makawa za a yi zaben gwamna a jihar Anambra

  • ‘Yan sandan Najeriya sun bayyana jajircewar su akan ganin zaben jihar Anambra na gwamnoni da za a yi a ranar 6 ga watan Nuwamban 2021 ya tabbata
  • Sifeta Janar na ‘yan Sanda, Usman Alkali Baba ya tabbatar wa da mazauna jihar ta kudu maso gabas cewa tabbas za ayi zaben kuma za su tabbatar da tsaro
  • Mutane da dama na yankin a razane su ke saboda tsoron ‘yan kungiyar IPOB da su ka dade su na tilasta jama’a zaman gida don a sako shugaban su

Legas - Sifeta janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, ya lashi takobin ganin ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro sun tabbatar zaben gwamnoni mai gabatowa a jihar Anambra ya tabbata.

An samu bayanai akan yadda za a gudanar da zaben a jihar Anambra a ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamba.

Read also

Mutane shida aka sace a jami’ar Abuja – Hukumar ‘yan sanda

Yayin wani taro da mataimakin sifeta janar na ‘yan sanda, Zone 2, Onikan, jihar Legas, Johnson Babatunde Kokumo, IGP din ya ce za a yi zaben.

IGP Usman Baba: Babu makawa sai an yi zaben gwamnan Anambra
Shugaban INEC, Farfesa Yakubu shima ya ce babu abin da zai hana a yi zaben Anambra. Photo credit: Pius Utomi Ekpei/AFP
Source: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Sun ta ruwaito yadda IGP din ya bayar da tabbaci inda ya ce:

“Mun tanadi jami’an tsaro kashi 2 a jihar Anambra. Kashi daya za su kula da jama’a yayin zaben don tabbatar da cewa ba a cutar da kowa ba.
“Bangare na 2 kuma za su dinga duba ayyukan ta’addanci na kungiyoyi kamar IPOB, ESN da sauran su, don gudun su shiga hakkin jama’a.”

Shugaban INEC ma ya ce za a yi zaben

A bangaren shugaban hukumar zabe mai zaman kan ta ta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ya tabbatar wa da mutanen jihar Anambra cewa tabbas za a yi zaben.

Ya kara da bayyana lokacin zaben inda ya ce za a yi ne a ranar 6 ga watan Nuwamba. Daily Trust ta yanko inda Farfesa Yakubu ya ke fadin hakan a Awka, ranar 2 ga watan Nuwamba.

Read also

2023: Tsohon Gwamnan Zamfara Yari ya magantu kan batun sauya sheka daga APC zuwa PDP

A cewar sa zaben zai tabbata ne da taimakon jami’an tsaro wadanda za su jajirce wurin ganin an yi zaben gaskiya da gaskiya cikin tsaro.

Dan takarar gwamna ya sharɓi kuka a bainar jama'a yayin yaƙin neman zaɓe a Anambra

A wani rahoton, dan takarar gwamna na jam'iyyar Zenith Labour Party (ZLP) da za a yi a ranar 6 ga watan Nuwamba, Dr Obiora Okonkwo, ya zubar da hawaye a yayin da ya ziyarci garin Okpoko don kaddamar da aikin titi na miliyoyin naira a ranar Laraba.

Aikin titin zai fara ne daga Ede Road, School Road/Awalite da Ojo street ya tsaya a Owerri road a garin Okpoko a karamar hukumar Ogbaru a jihar ta Anambra, Daily Trust ta ruwaito.

Okonkwo ya zubar da hawaye ne a lokacin da ya ga wata mata mai shayarwa mai shekaru 30 wadda ta fada cikin kwata bayan ta kasa bin titin saboda rashin kyawunsa.

Read also

Bayan lashe zabe, sabon shugaban matasan PDP ya magantu kan manufarsa akan APC

Source: Legit.ng

Online view pixel