Garba Shehu: Shari'ar Nnamdi Kanu za ta kawo karshen ta'addancin IPOB

Garba Shehu: Shari'ar Nnamdi Kanu za ta kawo karshen ta'addancin IPOB

  • Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya ce shari'ar Nnamdi Kanu za ta kawo karshen IPOB
  • A cewar mataimaki na musamman ga shugaban kasan, gwamnatin Buhari ce ke shawo kan matsalar Najeriya da ta dade
  • Ya yi wannan batun ne yayin martani ga jaridar The Economist wacce ke London kan wallafar da ta yi

Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa, ya ce shari'ar Nnamdi Kanu za ta kawo karshen ta'addancin kungiyar 'yan awaren Indigenous People of Biafra (IPOB).

Ya sanar da hakan ne yayin martani kan caccaka mai zafin da wata jaridar London, The Economist ta yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, Daily Trust ta wallafa.

Garba Shehu: Shari'ar Nnamdi Kanu za ta kawo karshen ta'addancin IPOB
Garba Shehu: Shari'ar Nnamdi Kanu za ta kawo karshen ta'addancin IPOB. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Jaridar ta caccaki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ta ce mulkinsa ya gaza shawo kan rashawa, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Buhari: Ba zan huta ba har sai na tabbatar Najeriya ba ta fama da kalubalen tsaro

A wata wallafa ta ranar 23 ga watan Oktoba, mujallar ta baje rundunar sojin Najeriya inda ta ce karfin rundunar a takarda kawai ya ke.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta yi ikirarin cewa, rundunar da ke da ma'aikatan bogi da ke karbar albashi ta na siyar da kayan aikin ta ga 'yan ta'adda domin haukata kasar nan.

Amma a wata takardar da Shehu ya fitar, ya ce jajircewa tare da kishin kasa irin na 'yan kasar Najeriya zai fitar da ita daga kalubalen da ta ke fuskanta.

Ya ce mujallar ta yi daidai da ta ce Najeriya na fuskantar kalubale amma sun hade ne ba saboda wannan gwamnatin ba. Wannan gwamnatin ce mai shawo kan su kuma babu gwamnatin da ta yi kokari kamar ta.

Mataimaki na musamman ga shugaban kasar ya ce kamawa da kuma gurfanar da Nnamdi Kanu shi ne tushen rushewar kungiyarsu.

Kara karanta wannan

Majalisa za ta mika ƙudurin ayyana 'yan bindiga da 'yan ta'adda gaban fadar shugaban kasa

Ya ce mulkin shugaban kasan ya na kara kaimi wurin tabbatar da an bayyana kungiyar IPOB a matsayin ta ta'addanci a gida da wajen Najeriya.

Shehu ya ce wannan lamarin zai kawo karshen duk wani kokarin 'yan ta'addan wurin samun tallafi daga kasashen ketare.

Kotu ta dage shari'ar Nnamdi Kanu, jami'an DSS sun iza keyarsa

A wani labari na daban, Jami'an tsaron farin kaya, DSS su sake iza keyar Nnamdi Kanu, shugaban 'yan awaren IPOB zuwa ma'adanarsu.

An gurfanar da Nnamdi Kanu a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja kan zargi bakwai da gwamnatin tarayya ke masa a ranar Alhamis, Daily Trust at ruwaito.

Kamar yadda TheCable ta wallafa, Kanu ya musanta zargin da ake masa da suka hada da cin amanar kasa da kuma ta'addanci.

Tawagar lauyoyin Kanu da suka samu jagorancin Ifeanyi Ejiofor, sun kalubalaci tsaresa a hannun hukumar DSS tare da bukatar a mayar da shi gidan yarin Kuje da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Kotu ta dage shari'ar Nnamdi Kanu, jami'an DSS sun iza keyarsa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel