Bayan harin masallaci, yan Bijilanti sun kashe mutum 9, sun ƙona gidaje a wata rugar Fulani a jihar Neja

Bayan harin masallaci, yan Bijilanti sun kashe mutum 9, sun ƙona gidaje a wata rugar Fulani a jihar Neja

  • Wasu da ake zargin yan Bijilanti ne sun hallaka aƙalla mutum 9 a wani harin ɗaukar fansa bayan harin Masallaci a jihar Neja
  • Rahoto ya nuna cewa maharan sun ƙone gidaje a wata rugar Fulani, bayan kashe dagacin Adogon Mallam da ɗan uwansa
  • Hukumar yan sanda ta tura jami'anta na musamman domin kame duk wani mai hannu a harin

Niger - Dailytrust ta rahoto cewa aƙalla mutum 9 ne suka rasa rayukansu a wani hari da aka kai rugar Fulani a ƙaramar hukumar Mashegu, jihar Neja.

Harin wanda ake zargin yan Bijilanti daga ƙauyen Maza Kuka ne suka aiwatar, ya faru tsakanin ranar Lahadi zuwa Litinin.

Hakazalika ana tsammanin na ɗaukar fansa ne kan abinda ya faru ranar 25 ga watan Oktoba a masallacin garin Maza-Kuka.

Yan bindiga
Bayan harin masallaci, yan Bijilanti sun kashe mutum 9, sun ƙona gidaje a wata rugar Fulani a jihar Neja Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa bayan harin ne, wasu yan banga suka hallaka dagacin garin Adogon-Mallam da ɗan uwansa.

Yadda lamarin harin ya faru

Ɗaya daga cikin waɗanda lamarin ya shafa, Shehu Mohammadu, yace:

"Yan bijilanti sun shigo ƙauyen mu, suka ƙona gidajen mu, sannan suka gudu. Matar ƙanina da ɗan jaririnta sun rasa ransu."
"Sun kuma kashe wani ƙani na, da ɗansa ɗan shekara 3, sun dai kashe mun yan uwana 7, kuma dole na gudu in ba haka ba nima su kashe ni."
"Mun bar ƙauyen, yanzun ina rayuwa a wani wuri mai nisa, kuma ba zan koma ƙauyen ba, domin nima kashe ni za su yi."

Wani shaidan da lamarin ya faru a idonsa, Alhaji Muhammadu Marike, yace yanzun haka yana gudun hijira ne a wajen jihar Neja.

"Banda harin da suka kashe dagacin garin Adogon Malam da ɗan uwansa, sun sake dawo wa. Sa'ar dana ci shine ɗaya daga cikinsu ya sanni, shine yace a kyale ni."
"Sun tafi da mutum 8, har yanzun babu wanda yasan inda suke. Mutanen mu sun tsere wuri mai nisa kamar Zaria da Kano."

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Kakakin yan sanda reshen jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, yace hukumarsu ta tura da ƙarin jami'an yan sanda domin kame masu hannu a harin.

Ya kuma yi kira ga al'umma su taimaka wa jami'an tsaro da bayanan sirri domin tabbatar da doka ta yi aikinta akan waɗan da suka aikata wannan ɗanyen aiki.

A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP ta yi kakkausan martani kan harin da yan bindiga suka kai jami'ar Abuja

Babbar jam'iyyar hamayya ta yi Allah wadai da harin, tare da kira a sako mutanen da aka kama cikin gaggawa domin su koma cikin iyalansu.

Jam'iyyar tace irin wanna hari a cikin Abuja, ya ƙara tabbatar da gazawar gwamnatin shugaban ƙasa Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel