Yadda mayakan ISWAP suka kashe jami'an yan sanda, suka kone motoci a sabon harin da suka kai Borno

Yadda mayakan ISWAP suka kashe jami'an yan sanda, suka kone motoci a sabon harin da suka kai Borno

  • Rahotanni daga Borno sun bayyana cewa mayaƙan ISWAP sun hallaka yan sanda uku da wata mace ɗaya a harin da suka kai Damboa
  • Maharan sun kone motocin jami'an tsaro, yayin da suka tilasta shiga barikin yan sanda a garin Damboa
  • Hakanan yan ta'addan sun kai hari ƙauyen Rann dake ƙaramar hukumar Kala-Balge a jihar Borno ranar Alhamis da dare

Borno - Jaridar Dailytrust ta ruwaito cewa aƙalla mutum huɗu, cikinsu harda yan sanda uku, sun rasa ransu yayin da mayaƙan ISWAP suka farmaki karamar hukumar Damboa, jihar Borno.

Wata majiya daga cikin jami'an tsaro ta bayyana wa manema labarai cewa yan ta'addan sun kai hari barikin yan sanda dake garin Damboa.

A cewar jami'in tsaron, maharan sun ƙone motoci aƙalla uku lokacin da suka ci ƙarfin jami'ai har suka kutsa cikin barikin.

Kara karanta wannan

Barayin da suka sace Liman da wasu 10 lokacin sallar Asuba a Neja Sun nemi a lale musu Miliyoyi

Jami'an yan sanda
Yadda mayakan ISWAP suka kashe jami'an yan sanda, suka kone motoci a sabon harin da suka kai Borno Hoto: lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Ya kuma kara da cewa yan ta'addan sun ƙone ofishin jami'an JTF, da na yan bijilanti a kan hanyar Biu, kuma sun ƙona motar sintiri.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shin an kashe fararen hula?

Majiyan yace wani harsashi da ba'a san daga inda ya hito ba ya sami wata yarinya kuma ta mutu nan take.

Jami'in yace:

"Zuwa yanzun mutum huɗu muka rasa, cikinsu har da yan sanda uku, da kuma wata yar ƙaramar yarinya da harsashi ya same ta."
"Sun kone motocin yan sanda uku da kuma motar sintiri ta jami'an sa'kai wato Bijilanti."

Mutane sun bar gidajen su

Rahotanni sun bayyana cewa ɗaruruwan fararen hula sun tsere daga gidajensu yayin da mayaƙan ISWAP suke gwabzawa da jami'an tsaro a garin Damboa.

Hakanan kuma wasu da ake zargin mayaƙan ISWAP ne sun kai hari ƙaramar hukumar Kala-Balge a jihar Borno, ranar Alhamis da daddare, amma sun kwashi kashinsu a hannun dakarun Soji.

Kara karanta wannan

Miyagun yan bindiga sun sake kai sabon hari jihar Zamfara, Sun kashe Mutane

Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 11:30 na dare a garin Rann, hedkwatar ƙaramar hukumar Kala-Balge a mazaɓar Borno ta tsakiya, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

A wani labarin kuma Bayan harin masallaci, Yan Banga sun hallaka Hakimi da ɗan uwansa a jihar Neja

Wasu yan banga sun ɗauki fansa kan harin da aka kai masallaci a jihar Neja, inda aka kashe mutane tare da sace wasu.

Rahoto ya nuna cewa yan bangan sun hallaka wani hakimi da ɗan uwansa bisa zarginsu da hannu a harin masallaci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel