Jam'iyyar PDP ta yi kakkausan martani kan harin da yan bindiga suka kai jami'ar Abuja

Jam'iyyar PDP ta yi kakkausan martani kan harin da yan bindiga suka kai jami'ar Abuja

  • Babbar jam'iyyar adawa PDP ta yi Allah wadai da harin yan bindiga a UNIABUJA, tare da sace malamai huɗu da wasu ƴaƴansu
  • Jam'iyyar tace irin wannan hari a cikin Abuja, ya ƙara tabbatar da gazawar gwamnatin shugaban ƙasa Buhari
  • PDP ta roki yan Najeriya su cigaba da yi wa mutanen dake hannun yan bindiga addu'ar samun kuɓuta

Abuja - Jam'iyyar PDP tace harin da yan bindiga suka kai jami'ar babban birnin tarayya Abuja, ta ƙara fito da gazawar gwamnatin shugaba Buhari fili.

Jaridar Punch ta rahoto yadda Maharan suka mamaye matsugunin malamai na jami'ar kuma suka sace mutum shida da safiyar Talata.

Babbar jam'iyyar hamayya ta yi Allah wadai da harin, tare da kira a sako mutanen da aka kama cikin gaggawa domin su koma cikin iyalansu.

UNIABUJA
Jam'iyyar PDP ta yi kakkausan martani kan harin da yan bindiga suka kai jami'ar Abuja Hoto: vangaurdngr.com
Asali: UGC

Wannan dai na ƙunshe ne a wata sanarwa da PDP ta fitar mai taken, 'Mun kaɗu da harin UNIABUJA' ɗauke da sa hannun kakakin ta na ƙasa, Kola Ologbondiyan.

Kara karanta wannan

A yi wa yan bindiga Afuwa kuma a ware kuɗaɗen ɗaukar nauyinsu, Sheikh Gumi ya magantu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Martanin PDP kan harin UNIABUJA

Wani sashin sanarwan yace:

"Jam'iyyar PDP ta yi Allah wadai da harin yan bindiga a jami'ar Abuja, wanda aka sace ma'aikata 4 da kuma wasu yayansu."
"Jam'iyya ta bayyana harin a matsayin na tsoro kuma ta bukaci maharan su sako waɗanda suka sace domin sake haɗuwa da iyalansu."
"Hakanan PDP na ganin ayyukan yan bindiga ƙarƙashin mulkin shugaba Buhari abun takaici ne, kuma yana ƙara tabbatar da gazawar gwamnatinsa."

Wane fata yan Najeriya ke da shi a kan Buhari.

PDP ta kara da cewa yan Najeriya na fatan bisa alƙawurran da shugaba Buhari ya yi, zaiyi amfani da ƙarfin ikonsa wajen kawo ƙarshen irin waɗan nan hare-haren.

"PDP na kira ga hukumomin tsaro kada su dogara da gazawar gwamnatin Buhari, amma su tashi tsaye, su binciko maharan sannan su ceto mutanen."

Kara karanta wannan

Mafi munin mulkin soja da aka taba yi a Najeriya yafi gwamnatin Buhari walwala da jin daɗi, Ortom

"Hakanan jam'iyyar ta roƙi yan Najeriya su cigaba da addu'ar fatan Allah ya kuɓutar da waɗan da aka sace daga sansanin yan bindiga."

A wani labarin kuma shahararriyar mai fafutukar nan Aisha Yesufu tace malamai sun fi shugabannin ƙasar nan lalacewa

A cewarta rashin kyakkyawan shugabanci yana taimaka wa malamai wajen cinikin kayan al'ajabi da kuma karfin magana.

Ta faɗi haka ne yayin da take martani kan maganar shugaban Deeper Christian Life Ministry, William Kumuyi, wanda ya gargaɗi kiristoci su daina zagin shugabanni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel