Yadda manyan gine-gine 8 suka ruguje a Najeriya cikin shekaru 15

Yadda manyan gine-gine 8 suka ruguje a Najeriya cikin shekaru 15

  • Rushewar gine-gine ya kasance abin da yake ta maimaituwa a cikin 'yan shekarun da suka gabata a laser nan, kama daga gidaje zuwa makarantu da ma majami'u
  • Akalla, an yi asarar rayuka sama da 100 a cikin shekaru 15 da suka wuce, inda aka yi asarar biliyoyin Naira na kudaden kasuwanci
  • Lamarin na baya-bayan nan wanda ya faru a ranar Litinin, 1 ga watan Nuwamba a Ikoyi, ya baiwa mazauna jihar Legas mamaki

Za a iya tunawa da rugujewar wani babban bene a ranar Litinin, 1 ga Nuwamba, 2021, a matsayin wata rana mai muni ga 'yan Najeriya.

Ginin da ya ruguje a titin Gerald da ke unguwar Ikoyi, wuri ne da ake gina gidaje na alfarma.

Sai dai abin takaici, ba wannan ne karon farko da ‘yan Najeriya ke fuskantar irin wanna, ba, suna mamakin ko me aka yi don hana rugujewar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Wani gini mai hawa-hawa ya sake ruftawa a jihar Legas

Yadda manyan gine-gine 8 suka ruguje a Najeriya cikin shekaru 15
Gini ya ruguje a Legas | Hoto: Bashir Ibrahim Idris
Asali: UGC

An samu karin aukuwar lamarin a tsawon shekaru, wannan yasa Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin fitattun hadurran da suka haifar da fargaba a fadin kasar.

Shekarar 2006

Shekarar 2006 ana daukarta a matsayin daya daga cikin mafi muni ta fuskar rushewar gine-gine kamar yadda rahotonni suka bayyana aukuwar wasu hadurra uku a cikin shekarar.

Na farko ya faru ne a ranar Laraba, 22 ga Maris, 2006 a ginin bankin bunkasa masana’antu na Najeriya bayan gobara ta kone gidaje biyu a ginin a farkon watan.

Rahoton ya nuna cewa, iska mai karfi a lokacin da aka yi tsawa ta sa ginin ya kife.

A ranar 18 ga Yuli, 2006, wani rukunin gidaje mai hawa hudu ya ruguje a Legas, inda akalla mutane 25 suka mutu.

Kara karanta wannan

Bayan tsige shi, 'yan sanda sun kame shugaban majalisar dokokin Filato da tawagarsa

Rahoton ya nuna cewa ginin bai kai shekara uku ba wanda ya kunshi gidaje 36.

Wani lamarin kuma ya sake aukuwa a cikin watan Nuwambar shekarar 2006, bayan da wani gini mai hawa uku da ba a gama shi ba ya ruguje. An bayar da rahoton mutuwar ma’aikatan gine-gine biyu.

Shekarar 2014

A ranar 12 ga Satumba, 2014, wani masaukin baki da ke cikin cocin Synagogue da ke unguwar Ikotun-Egbe a jihar Legas ya ruguje gaba dayansa.

Lamarin dai ya haifar da firgici yayin da aka ce sama da mutane 115 sun mutu inda 84 daga cikinsu ‘yan kasar Afirka ta Kudu ne.

Shekarar 2016

A ranar 8 ga watan Maris, 2016, wani gini mai hawa biyar ya ruguje yayin da ake kan aikin gininsa a yankin Lekki da ke Legas a Najeriya.

Rahoto ya kuma nuna cewa akalla mutane 34 ne suka mutu yayin da wasu 13 kuma aka ciro su daga ginin da ya ruguje da ransu a wani aikin ceto da aka kawo karshensa a ranar 10 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Dinbin mutane sun makale carko-carko yayin da gini mai hawa 20 ya ruguje a Najeriya

Haka kuma a shekarar 2016, wani gini ya ruguje a ranar 10 ga watan Disamba bayan rugujewar rufin cocin Reigners Bible Church International, wata kungiyar yada addinin kirista a garin Uyo dake jihar Akwa Ibom a Najeriya, a lokacin da ake nada wani Bishop na yankin.

Akalla mutane 23 aka tabbatar sun mutu a lamarin, yayin da wasu rahotanni suka bayyana adadinsu ya kai 160.

Makarantar Firamare ta rushe a 2019

A ranar 13 ga watan Maris, 2019, wani gini mai hawa uku na makarantar firamare a unguwar Ita Faaji da ke birnin Legas, a Najeriya ya ruguje, inda mutane 20 suka mutu tare da ikkata sama da 40.

Gwamnan jihar Legas a lokacin da lamarin ya faru, Akinwunmi Ambode ya ce makarantar firamaren ta mamaye ginin ba bisa ka'ida ba saboda an yi wa ginin rajista ne a matsayin gidan zama.

Shekarar 2021

Na baya-bayan nan shi ne ranar Litinin, 1 ga Nuwamba, 2021, lamarin da ya zuwa yanzu ya lakume rayuka sama da 6 tare da labarin cewa mai ginin ya makale a cikinsa.

Kara karanta wannan

Kogi: 'Yan bindiga sun sheke rayuka 6, sun babbaka fadar Sarki da wasu gidaje masu yawa

Gwamnan Legas ya kori daraktan kula da gine-gine bayan rugujewar bene mai hawa 22

Jaridar The Naation ta ruwato cewa, gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya dakatar da babban manajan hukumar kula da gine-gine ta jihar Legas (LASBCA) Gbolahan Oki.

Gwamnan ya sha alwashin gano abin da ya faru tare da hukunta wadanda ake tuhuma da hannu a rugujewar bene mai hawa 22 da ya ruguje a Ikoyi ta jihar.

Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai da Dabaru Gbenga Omotoso, ya fitar, ta ce gwamnatin jihar za ta kafa wani kwamiti mai zaman kansa da zai binciki rugujewar ginin na kan titin Gerrard, Ikoyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel