Zamfara: Jerin kasuwanni 7 da Matawalle ya bada umurnin a buɗe su

Zamfara: Jerin kasuwanni 7 da Matawalle ya bada umurnin a buɗe su

  • Gwamnatin jihar Zamfara ta amince da kara bude kasuwanni 7 na mako a ranar Litinin, 1 ga watan Nuwamba wadanda dama ta rufe su don kawo garanbawul akan matsalar tsaro a jihar
  • Kwamishinan labarai na jihar, Alhaji Ibrahim Dosara ne ya bayyana hakan a ranar Litinin ta wata takarda a Gusau inda ya lissafo kasuwannin da za a bude
  • Kamar yadda kwamishinan ya bayyana, bisa dokar jihar, har yanzu ba a amince da ci gaba da siyar da dabbobi ba don yin hakan karya doka ne, Kuma ya ce gwamnati za ta kara rufe kasuwannin idan aka karya dokoki

Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta amince da kara bude kasuwanni 7 wadanda da can ta umarci a rufe su don kawo gyara akan matsalolin tsaron da jihar ta ke fama da su.

Kara karanta wannan

Gwamnan Gombe ya bukaci a kwashe tubabbun 'yan Boko Haram a kaisu jami'ar soji

Bisa ruwayar The Punch, Kwamishinan labarai na jihar, Alhaji Ibrahim Dosara ne ya bayyana hakan ta wata takardar ranar Litinin a Gusau.

Matawalle ya bada umurnin bude kasuwanni 7 a fadin jihar Zamfara
Gwamna Matawalle ya bada umurnin bude kasuwanni 7 a fadin jihar Zamfara. Hoto: NewsWireNGR
Asali: Facebook

Jaridar NewsWireNGR ma ta ruwaito yadda kwamishinan ya ce:

“Wannan sanarwa ce ga kowa, bayan ganin yadda tsaro ya fara kankama a jihar da kuma rokon gwamnati da jama’a su ka dinga, gwamnati ta amince da kara bude kasuwannin mako daga ranar Litinin, 1 ga watan Nuwamban 2021.”

Kasuwannin da za a bude sune:

  1. Kasuwar Nasarawar Burkullu ta karamar hukumar Bukkuyum,
  2. Kasuwar Talata Mafara da ke karamar hukumar Talata Mafara
  3. Kasuwar Gusau ta karamar hukumar Gusau.
  4. Kasuwar Shinkafi ta karamar hukumar Shinkafi
  5. Kasuwar Daji ta karamar hukumar Kaura Namoda
  6. Kasuwar Nasarawar Godel ta karamar hukumar Birnin Magaji da
  7. Kasuwar Danjibga ta karamar hukumar Tsafe

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta amince da biyan kudin kammala titin Gombe zuwa Biu

Gwamnati ta dakatar da bude kasuwannin dabbobi

Kamar yadda takardar ta zo, gwamnati ta wajabta ci gaba da rufe kasuwannin dabbobi, don haka kada wani ya kuskura ya karya dokar jihar.

Dosara ya kara da cewa:

“Kada a kuskura a ga mutane da makamai a kasuwannin kuma kada wani ya tayar da hayaniya da sunan kungiya ko makamancin hakan.”

Don haka ne gwamnati ta bukaci taimakon jami’an tsaro don su tabbatar da tsaro a kasuwannin kuma su tabbatar sun hana yawo da makamai a kasuwannin.

Kwamishinan ya ja kunnen jama’a akan karya wata dokar da gwamnatin jihar ta shimfida inda ya ce matsawar hakan ta faru za a sake garkame kasuwannin.

Labari da ɗuminsa: An kashe Dogo Giɗe, ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga da ya daɗe yana addabar jihohin arewa

A baya, Legit ta kawo muku wani rahoto da ya ce an kashe hatsabibin shugaban 'yan bindiga Dogo Gide.

Kara karanta wannan

Buhari ya kashe sama da N45bn domin inganta rayuwar Katsinawa, Masari

An kashe shi ne a dajin Kuyanbana da ke jihar Kaduna kamar yadda PRNigeria ta wallafa.

A watan Maris na shekarar 2018, Gide ya kashe hatsabibin shugaban yan bindiga a wannan lokacin, Buharin Daji, bayan hakan ne ya zama shugaban yan bindigan yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel