Rahoto: Yadda yaro karami cikin 'yan ta'addan ISWAP ya hallaka sojojin Najeriya

Rahoto: Yadda yaro karami cikin 'yan ta'addan ISWAP ya hallaka sojojin Najeriya

  • Wani bidiyo ya bayyana, inda aka ga wani yaro karami yana kashe wasu jami'an sojojin Najeriya
  • Rahoton ya bayyana cewa, yaron yana cikin 'yan ta'addan kungiyar ISWAP da ta addabi jihar Borno
  • Masu sharhi da masana harkokin tsaro na duniya sun bayyana bacin ransu da irin wannan mummunan barna

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, kungiyar ta'addanci ta ISIS ta fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna wani yaro cikin 'yan ta'addan yana kashe wasu sojojin Najeriya biyu.

A cikin gajeren faifan bidiyon, an nuna wani karamin yaro wanda dan kungiyar ISWAP ne bijararren yankin kungiyar Boko Haram da ya balle, yana aiwatar da hukuncin kisa ga sojojin da aka kama a Arewa maso Gabas.

Yaron ya harbe sojojin ne da bindiga kirar AK-47.

Kara karanta wannan

Yadda Tarayyar Turai ta kashe £130m wajen tallafawa 'yan gudun hijira a Borno

Rahoto: Yadda yaro karami cikin 'yan ta'addan ISWAP ta hallaka sojojin Najeriya
'Yan ta'addan ISWAP | Hoto: saharareporters.com
Asali: Twitter

Sai dai kungiyar ISWAP ta nuna wani harin bam da ake kyautata zaton ya faru ne a Mallam Fatori da ke jihar Borno duk da cewa ba a iya tantance ainihin ranar da hakan ya faru ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Irin wannan bidiyo na tashin bam wata dabara ce da mayakan ke amfani da su a wasu lokuta don nuna tasirinsu.

Bidiyon mai suna "Makers of Epic Battles" ya kuma shafi wasu hare-hare daga yakin bazara na ISWAP a jihohin Borno da Yobe a 2021.

Tomasz Rolbiecki, wani mai bincike kan hare-haren kungiyar ISWAP a duk duniya, ya bayyana faifan a matsayin "mummuna."

SaharaReporters ta ruwaito cewa, Rolbiecki ya yi rubuta a shafinsa na sada zumunta cewa:

"Babu wasu kalmomi da za su kwatanta munin abin."

Ya ci gaba da cewa:

“Gaba daya, faifan bidiyon ya shafi hare-haren da kungiyar ISWAP ta yi a lokacin bazara a arewacin Borno da Yobe, duk da cewa akwai faifan bidiyo daga yankin kudu maso gabas da kudu maso yammacin jihar Borno.

Kara karanta wannan

Cikin hotuna, jiragen yaƙin NAF sun yi wa taron ƴan Boko Haram ruwan wuta, sun kashe 37 a Sambisa

“Yawancin bidiyon an buga su a rahotannin hoto tun kafin a fitar da wannan bidiyon. Daesh ta kwashe shekaru tana yi. Sai dai, akwai kuma wasu sabbin abubuwa."

Rahoton ya ce, ISWAP na amfani da wasu dabarun kai hare-hare na APC na lokaci mai tsawo.

Ya kara da cewa:

“Harin Gajiram shi ne na gaba. Yana da wuya a gane wanne ne tunda akwai da yawa a cikin shekarar da ta gabata, kuma ba a fitar da faifan a baya ta kowace hanya ba."

Hakazalika, an nuna wani faifan bidiyo daga Geidam ta Jihar Yobe, harin da aka kai a ranar 23 ga Afrilu, inda ISWAP ta kafa tutarta a garin.

ISWAP ta hallaka wasu jiga-jigan kwamandojin Boko Haram da mabiyansu 18

Jaridar PRNigeria ta ruwaito cewa an kashe manyan jiga-jigan kungiyar Boko Haram guda biyu, Amir Modou Marte da Amir Moustapha Baga.

An kawar da su ne a wani kwanton bauna da mayakan abokan hamayyarsu na ISWAP suka yi a ranar Lahadi 24 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Rahoto: Masu ƙera wa Boko Haram bama-bamai sun koma dazukan Kudancin Kaduna

An tattaro cewa wasu 'yan ta'adda 15 na daga cikin wadanda kungiyar Boko Haram ta kashe a lokacin kwanton baunar da suka yi a Toumboun Gadura'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel