Jerin mutum 3 da suka sha mugun kaye a zaben shugabannin jam'iyyar PDP

Jerin mutum 3 da suka sha mugun kaye a zaben shugabannin jam'iyyar PDP

  • A ranar Asabar ne jam'iyyar PDP ta zabi sabbin shugabannin kwamitin ayyukan ta kafin zuwan zaben 2023
  • Daga cikin mukamai 21 , mukamai 3 ne kadai aka yi karon batta kuma aka buga kafin a fitar da gwani daga cikin 'yan takarar
  • Akwai mukaman mataimakan shugabannin jam'iyyar a yankunan arewa da kudu da kuma kujerar shugaban matasa na kasa

Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta zabi sabbin shugabannin kwamitin ayyuka na kasa wadanda za su jagoranci jam'iyyar kafin zuwan gagarumin zaben 2023.

Mukamai uku kacal daga cikin mukamai 21 na kwamitin ayyukan ne aka fafata wurin samun kujerar, yayin da sauran mukaman an zabi wadanda suka dace da kujerar ne.

Jerin mutum 3 da suka sha mugun kaye a zaben shugabannin jam'iyyar PDP
Jerin mutum 3 da suka sha mugun kaye a zaben shugabannin jam'iyyar PDP. Hoto daga thecable.ng
Source: UGC

A wannan rahoton, Legit.ng ta lissafo muku manyan mutum 3 da suka nemi kujerun mukami kuma aka buga su da kasa.

Read also

Cikin hotuna: Matashi mai shekaru 25 da ya lashe kujerar shugaban matasan PDP

1. Hajiya Inna Ciroma

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A mukamin mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa daga arewa, Umar Damagum, tsohon dan takarar kujerar gwamnan daga jihar Yobe, ya samu kuri'u 2,222 inda ya lallasa Inna Ciroma, tsohuwar ministar mata daga jihar Borno wacce ta samu kuri'u 365.

2. Prince Olagunsoye Oyinlola

Olagunsoye Oyinlola, tsohon gwamnan jihar Osun, ya fadi a mukamin mataimakin shugaban jam'iyya daga kudu da ya nema inda ya samu kuri'u 705.

Abokin hamayyarsa, Taofeek Arapaja, tsohon mataimakin gwamnan jihar Oyo, ya samu kuri'u 2,004.

3. Usman Elkudan

Daga cikin 'yan takara biyu daga jihar Kaduna kan mukamin shugaban matasa na kasa na jam'iyyar, Muhammad Kadade Suleiman ya samu kuri'u 3072 inda ya lallasa Usman Elkudan wanda ya samu kuri'u 219.

Kotu ta hana Secondus dakatar da gangamin taron PDP na ƙasa

Read also

Ana saura mako daya zabe Gwamna, yan majalisa 3 sun sauya sheka APC

A wani labari na daban, Uche Secondus, dakataccen shugaban jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, na ƙasa bai yi nasara ba a yunkurinsa na hana yin gangamin taron jam'iyyar na ƙasa, TVC News ta ruwaito.

Secondus ya garzaya kotun daukaka kara ne inda ya ke ƙalubalantar dakatar da shi da aka yi a matsayin shugaban Jam'iyyar na kasa.

Ya kuma shigar da wata bukatar a gaban kotu yana neman a hana ta yin gangamin taron ta Na kasa da ta shirya yi a ranakun 30 da 31 ga watan Oktoba.

Source: Legit.ng

Online view pixel