Kishi Kumallon Mata: Wata Budurwa ta daba wa Saurayinta wuka daga duba WhatsApp dinsa

Kishi Kumallon Mata: Wata Budurwa ta daba wa Saurayinta wuka daga duba WhatsApp dinsa

  • Wata dalibar kwalejin fasaha ta caka wa saurayinta wuka bayan duba irin firar da yake da wasu mata a WhatsApp
  • Dalibar dake karatun aikin jarida a kwalejin jihar Delta, ta aikata wannan aika-aika ne a ranar Laraba da ta gabata
  • Saurayin yace budurwan tasa ta ɗauki wayarsa ne lokacin yana bacci, ba zato yaji an daba masa wuka a hannunsa na dama

Delta - Wata ɗaliba dake koyon aikin jarida a kwalejin fasaha ta jihar Delta, Ogwashi-Uku, da aka fi sani da Chidimma ya daba wa saurayinta Daniel Johnson, wuka saboda yana fira da wata a WhatsApp.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa ta daba wa saurayin wuka ne ranar Laraba 27 ga watan Oktoba, amma ya tsira daga lamarin.

Read also

Bidiyon budurwar da ta yarfa saurayinta cikin mutane yayin da ya yi mata tayin aure, ta ƙwace zoben ta jefar a ƙasa

Kwalejin fasaha
Kishi Kumallon Mata: Wata Budurwa ta daba wa Saurayinta wuka daga duba WhatsApp dinsa Hoto: punchng.com
Source: UGC

Da yake bayyana halin da ya shiga bayan samun sauki, Johnson, yace budurwan tasa ta duba sakonnin shi na WhatsApp lokacin da yake bacci.

Me budurwan da gani a WhatsApp ɗin?

A jawabina saurayin yace:

"Ina bacci lokacin da ta ɗauki wayana tana bincike, ta buɗe Whatsapp ɗina ta karanta hira ta da wata yarinya daban."
"Daga nan sai ta daɓa mun wuƙa a hannun dama, na tashi da yankar wuƙa a hannu na, na nemi mutane su taimaka mun kafin abun ya yi muni."
"Maƙota na ne suka cece ni, kuma aka kira yan sanda suka tafi da ita ofishin su na Asaba. Gaskiya na yi sa'a da na cigaba da rayuwa."

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Da aka tuntuɓe shi domin jin halin da ake ciki, Kakakin yan sanda reshen jihar, DSP Bright Edafe, ya shaida wa manema labarai cewa har yanzun rahoton bai zo hedkwatar yan sanda ba.

Read also

Tsoro da zaman dardar: Yadda shirin NYSC ya zama abin tsaro ga 'yan bautar kasa

A wani labarin kuma wata matar aure ta bayyana yadda mijinta ke jibgarta kuma ya mata barazanar taba ta da duniya

Wata mata ta garzaya kotu tana neman alkali ya shiga tsakaninta da mijinta saboda yana barzanar kashe ta da yayanta.

Matar tace mijin nata ba shi da imani, da zaran sun samu yar matsala ƙarama, sai ya kama jibgarta.

Source: Legit.ng

Online view pixel