Bidiyon yadda budurwa ta ƙi amincewa da tayin auren saurayi, ta ƙwace zoben ta jefar a ƙasa

Bidiyon yadda budurwa ta ƙi amincewa da tayin auren saurayi, ta ƙwace zoben ta jefar a ƙasa

  • Bidiyon wata daliba da ta kammala jami'ar TASUED ya janyo cece-kuce bayan ta ki amincewa ta tayin aure da saurayinta ya yi mata a bainar jama'a
  • Budurwar ta karbi zobe daga hannun saurayinta da ya durkusa a gwiwoyinsa, sannan ta jefar a kasa yayin da abokan karatunta ke tuntsura dariya
  • Saurayin nata da ta ki amincewa da tayin aurensa ya cigaba da kasancewa a gwiwoyinsa har sai da wasu mutane suka daga shi

Bidiyon yadda wata budurwa wacce ita da saurayin ta su ka kammala jami’a ta ki amsar tayin auren sa a bainar jama’a ya janyo cece-kuce.

Sun kammala jami’ar ilimi ta Tai Solarin da ke Ijebu-Ode ne, a ranar bikin gama jami’ar saurayin ya durkusa har kasa rike da zobe a gaban budurwar kamar yadda bidiyon ya nuna.

Read also

Soyayya dadi: Yadda gimbiya ta bar masarauta da makudan miliyoyi ta auri talaka tukuf

Bidiyon yadda budurwa ta ƙi amincewa da tayin auren saurayi, ta ƙwace zoben ta jefar a ƙasa
Budurwa ta ƙi amincewa da tayin auren saurayi, ta ƙwace zoben ta jefar a ƙasa. Hoto: @ijeomadaisy
Source: Facebook

A bidiyon wanda Ijeoma Daisy ta wallafa a shafin ta na Instagram an ga yadda budurwar ta amshi zoben da ga hannun saurayin na ta ta jefar kuma ta bar wurin.

Abokan karatun su sun taru a wurin da lamarin ya faru inda saboda takaici saurayin ya kasa mike wa tsaye.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Saidai wata budurwa da take kusa da shi ne ta tallafa ma sa ya mike cike da takaici.

Wannan bidiyon ya janyo cece-kuce inda wata Callmeada1 ta yi tsokaci da:

“Gaskiya abin nan ya ba ni dariya...Samari ku dinga tabbatar da kudirin budurwar ku don gudun irin wannan abu. Gaskiya wannan tozarci ne."

Kfrosh ya ce:

“Yaron wawa ne, daga gama makaranta sai batun aure. Yarinyar ma ta na da wayau."

Weightlossbyslvia ta ce:

“Gara da ba ta ga idon mutane ta amince da zoben ba. Saboda maganar mutane ta na iya ja ka amince da abinda ba ka yi niyya ba.”

Read also

Sabon hari: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

Iyaalajor ta ce:

“Daga gama makaranta, za ka fara batun aure? Babu wani tsari? So kake ka wahalar da ni? Nemo kudi, fara yin bautar kasa tukunna."

Everywomansecret ta yi tsokaci da:

“Yaron ba ya da tunani. Ya na kokarin yin aure ba tare da ya nemo aiki ba. Ba lallai yarinyar ta zama zabin auren shi a nan gaba ba."

Shugaban wurin aiki ya ba na ƙasa da shi da ke tattaki zuwa wurin aiki kyautar mota

A baya, kun ji wani matashi, Walter, ya yi tattakain mil 20 a ranar sa ta farko ta zuwa wurin aiki. Motar sa ta samu matsala ana gobe zai fara zuwa aikin hakan ya sa ya yanke wannan shawarar.

Kafin safiyar, ya yi kokarin tuntubar abokan sa amma babu alamar zai samu tallafi saboda ya sanar da su a kurarren lokaci kamar yadda Understanding Compassion ta ruwaito.

Read also

Kano: Mai kwacen waya ya halaka tela mai shekaru 30 a adaidaita sahu

Daga nan ne ya yanke shawarar fara tattaki tun karfe 12am don isa wurin aikin da wuri. Matashin bai bari rashin abin hawan ya dakatar da shi ba.

Source: Legit.ng News

Online view pixel