FG ta kara wa'adin rufe layikan wayoyin da ba a hada da NIN ba

FG ta kara wa'adin rufe layikan wayoyin da ba a hada da NIN ba

  • Gwamnatin tarayya ta sanar da kara wa'adin hada layikan wayoyi da lambar katin dan kasa ta NIN
  • Kamar yadda ma'aikatar sadarwa ta sanar, gwamnatin tarayya ta dage kafa har zuwa 31 ga Disamba
  • Hakan ya biyo bayan rokon alfarma da kamfanonin layika da masu ruwa da tsaki suka yi ga gwamnatin tarayyan

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta sake tsawaita wa'adin da ta diba na hada layikan wayoyi da lambar katin dan kasa zuwa ranar 31 ga watan Disamba mai zuwa.

Daily Trust ta wallafa cewa, wannan ne karo na bakwai da gwamnati ta dage lokacin datse layikan da ba a hada da lambar katin dan kasa ba, wanda ta ce hakan zai dakile hauhawar rashin tsaro a kasar nan.

Read also

Ba ni da hannu a dirar mikiya da jami'an tsaro suka yi a gidan Mary Odili, Malami

FG ta kara wa'adin rufe layikan wayoyin da ba a hada da NIN ba
FG ta kara wa'adin rufe layikan wayoyin da ba a hada da NIN ba. Hoto daga dailytrust.com
Source: UGC
"Mai girma ministan sadarwa da tattalin arziki mai dogaro da fasahar zamani, Farfesa Isah Ali Ibrahim ya sanar da cewa gwamnatin tarayya ta kara lokaci kan wa'adin da ta diba na toshe layikan da ba a hada da lambar katin dan kasa ba.
"Ana kira ga 'yan kasa da mazauna kasar nan da su tabbatar da sun hada kafin nan da karshen shekarar nan," wata takarda da mai magana da yawun hukumar sadarwa ta kasa Ikechukwu Adinde da mai magana da yawun NIMC, Kayode Adegoke suka sa hannu.

Takardar ta ce wannan hukuncin karin wa'adin lokacin ya biyo bayan rokon da masu aiki da layikan wayoyi da kuma sauran masu ruwa da tsaki suka dinga yi ne, Daily Trust ta wallafa.

Takardar ta ce sun bukaci a kara wa'adin ne saboda a tabbatar da cewa an bi umarnin gwamnti domin gujewa toshe layikan.

Read also

Gwamnatin Buhari ta amince da biyan kudin kammala titin Gombe zuwa Biu

Takardar ta ce: "Kara wa'adin zai samar da damar yi wa 'yan Najeriya da ke kauyuka rijista, kasashen waje, makarantu, asibitoci, wuraren bauta, bakin haure da sauransu wadanda a farko duk basu yi ba."

Rufe layikan waya: 'Yan Najeriya sun koka a kan N20 na duba NIN

A wani labari na daban, bayan gwamnatin tarayya ta bayar da sanarwa a kan rufe duk wani layin waya wadanda ba a hada shi da lambar katin dan kasar mai shi ba, wato NIN, daga ranar 30 ga watan Disamba.

Mutane da dama sun rikice a kan N20 din da za su yi amfani da ita don duba NIN din ta hanyar kiran *346#, Vanguard ta wallafa.

Umarnin rufe layin wayar yazo ne bayan taron gaggawa da masu ruwa da tsaki suka yi na kamfanin sadarwa da ministan sadarwa, Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami, a ranar Litinin, 14 ga watan Disamban 2020.

Read also

Take hakkin dan Adam: UN ta aiko wa Najeriya wasika, ta bukaci bayanai 5 game da kamen Kanu

Source: Legit.ng

Online view pixel