Tashar Ruwa 1 da Shugabannin Najeriya 3 Suka Amince da Gina Ta amma har Yanzu ba a Gama ba

Tashar Ruwa 1 da Shugabannin Najeriya 3 Suka Amince da Gina Ta amma har Yanzu ba a Gama ba

  • Gwamnatocin Goodluck Jonathan, Muhammadu Buhari da Bola Tinubu sun ɗauki matakai daban-daban na goyon bayan aikin tashar jirgin ruwan Ibom
  • Tinubu ya amince da buƙatar Gwamna Umo Eno yayin wani gangamin APC a Uyo ranar 6 ga Nuwamba, 2026
  • Duk da amincewar gwamnatocin uku, har yanzu ba a mayar da aikin tashar zuwa wani wuri da ke gudanar da harkokin jigilar kaya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Akwa Ibom - Shirin gina babbar tashar jirgin ruwa ta Ibom Deep Sea Port a jihar Akwa Ibom ya samu goyon bayan gwamnatin tarayya a ƙarƙashin gwamnatoci uku a jere, amma har yanzu ba ta fara aiki ba.

Wannan lamari ya jawo tambayoyi kan dalilin da ya sa amincewar gwamnati ba ta haifar da aiwatar da aikin a zahiri ba.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Matashin da ya auri mata 2 rana 1 ya rasu a wani yanayi mai cike da al'ajabi

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a wurin yakin neman zaben APC a jihar Rivers
Source: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa shugabannin kasa uku ne suka amince da aikin gina wannana tashar ruwa, amma har yanzu ba ta fara aikin jigilar kaya yadda ya kamata ba.

Gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan ta amince da aikin a a 2012, yayin da ta Muhammadu Buhari ta amince a a 2020, sai kuma yanzu Shugaba Bola Tinubu ya bi sahu a 2026.

Jawabin Tinubu a gangamin APC

Amincewa ta baya-bayan nan ta zo ne ranar Juma’a, 6 ga Nuwamba, lokacin da Tinubu ya amince a bainar jama’a da buƙatar da Gwamna Umo Eno ya gabatar masa yayin gangamin kamfen APC a Uyo.

Da yake mayar da martani kan buƙatar gwamnan, shugaban ƙasar ya ce:

“An amince da buƙatarku ta gina tashar jirgin ruwa ta Ibom Deep Sea Port. Tashar za ta kawo ci gaban tattalin arziki da fa’idodi ga jama’a, kamar yadda gwamnan ya bayyana.”

Kara karanta wannan

Akpabio ya fadi miliyoyin kuri'un da zai samawa Tinubu a 2027

Fadar Shugaban Ƙasa ma ta fitar da sanarwa tana tabbatar da amincewar, inda ta bayyana tashar da aka tsara ginawa a matsayin wani babban ginshiƙi da zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki da wadata a Akwa Ibom da yankin Kudu-maso-Kudu.

Sai dai sanarwar ta jawo suka, musamman ganin cewa aikin ya kasance cikin tsare-tsaren bunƙasa ƙasa da sanarwar gwamnatoci daban-daban, amma har yanzu ba a ga wani gagarumin aikin gine-gine a wurin ba.

Matakin gwamnatin Jonathan

A ƙarƙashin gwamnatin Jonathan, gwamnatin tarayya ta ɗauki matakin farko da aka samu sahihin bayani a kansa na bunƙasa tashar Ibaka Deep Seaport a ranar 18 ga Satumba, 2012.

A ranar ne Ministan Sufuri na lokacin, Sanata Idris Umar, ya ƙaddamar da kwamitin gwamnatin tarayya mai kula da bunƙasa aikin da jagorantar aiwatar da shi.

Amincewar gwamnatin Buhari

Shekaru takwas bayan haka, Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) a ƙarƙashin gwamnatin Buhari ta amince da fara aikin gina tashar Ibom Deep Seaport a ranar 16 ga Disamba, 2020.

An sanar da matakin washegari ta bakin Kwamishinan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa na jihar Akwa Ibom na lokacin, Ini EmemObong.

Ya ce amincewar ta biyo bayan ƙoƙarin da gwamnatin tsohon Gwamna Udom Emmanuel ta daɗe tana yi domin ganin an aiwatar da aikin.

Kara karanta wannan

Abin da Gwamnatin tarayya take so mutum ya yi idan aka tura masa saƙon tallafin N50,000

EmemObong ya ce:

“Wannan amincewa ta zo ne bayan ƙoƙarin da gwamnatin Udom Emmanuel ta daɗe tana yi domin ganin an tabbatar da wannan buri da aka daɗe ana jira.”

Sabuwar amincewar Tinubu

Sanarwar Tinubu ta baya-bayan nan ta sake buɗe muhawara kan matsayin aikin da kuma dalilin da ya sa matakan da gwamnatocin baya suka ɗauka ba su haifar da tashar jirgin ruwa da ke aiki ba.

Ko da yake gwamnatocin ukun sun ɗauki matakai na goyon bayan aikin, matakan da kowannensu ya ɗauka sun bambanta.

Gwamnatin Jonathan ta ƙaddamar da kwamitin bunƙasa aikin a 2012, yayin da Majalisar Zartarwa ta Tarayya a ƙarƙashin Buhari ta amince da fara aikin a 2020.

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a wurin taron yakin neman zaben shugaban kasa na APC a Akwa Ibom Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A nasa ɓangaren, Tinubu ya sanar da amincewarsa da aikin amma bai bayar da cikakken bayani kan yadda za a samar da kuɗin aikin ba, tsarin bayar da kwangila ko shirye-shiryen fara gine-gine ba.

Saboda haka, sanarwar ta baya-bayan nan ta bar wata muhimmiyar tambaya ba tare da amsa ba: Me ya sa aikin da ya shafe sama da shekaru goma yana cikin tsare-tsaren gwamnatin tarayya har yanzu bai zama tashar jirgin ruwa mai zurfi da ke gudanar da harkokinta ba?

Kara karanta wannan

Babbar kotu ta karɓi shaidu kan waɗanda ake zargi da yunkurin yi wa Tinubu juyin mulki

Tinubu ya kare darajar Naira

A wani labarin, kun ji cewa shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubuya kare yadda Naira ta kasance a ƙarƙashin gwamnatinsa inda ya fadi fa'idojin da aka samu kan haka.

Tinubu ya bayyana cewa da ba don sauye-sauyen da ya kawo a harkar musayar kuɗaɗen waje ba, da kuɗin ƙasar ya rasa darajarsa gaba ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262