Rufe layikan waya: 'Yan Najeriya sun koka a kan N20 na duba NIN

Rufe layikan waya: 'Yan Najeriya sun koka a kan N20 na duba NIN

- A ranar Litinin minista Pantami ya bayar da umarnin duba NIN ta hanyar *346#, ko kuma a rufe layin wayar mutum

- Tun bayan nan 'yan Najeriya suka shiga caccakar ma'aikatar sadarwa a kan N20 din da za a cire musu idan za su duba NIN

- Wasu gani suke yi wata sabuwar hanyar damfara ce ma'aikatar ta bullo da ita, don haka suka yi ta korafi wasu suka ki yi

Bayan gwamnatin tarayya ta bayar da sanarwa a kan rufe duk wani layin waya wadanda ba a hada shi da lambar katin dan kasar mai shi ba, wato NIN, daga ranar 30 ga watan Disamba.

Mutane da dama sun rikice a kan N20 din da za su yi amfani da ita don duba NIN din ta hanyar kiran *346#, Vanguard ta wallafa.

Umarnin rufe katin wayar yazo ne bayan taron gaggawa da masu ruwa da tsaki suka yi na kamfanin sadarwa da ministan sadarwa, Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami, a ranar Litinin, 14 ga watan Disamban 2020.

Rufe layikan waya: 'Yan Najeriya sun koka a kan N20 na duba NIN
Rufe layikan waya: 'Yan Najeriya sun koka a kan N20 na duba NIN. Hoto daga @Vanguardngrnews
Source: Twitter

KU KARANTA: Tsohuwa mai shekaru 81 ta rasu, ta bar wa makwabta gadon N2.8bn

Bayan doguwar tattaunawar ne aka samar da shawarar wajabta hada layuka da NIN. Daga nan ne 'yan Najeriya suka yi ta cece-kuce a Twitter.

Wani MrOdanz cewa yayi, "Lallai wannan salon damfara ne. A kalla mutane miliyan 100 za su yi, idan ka kirga N20 sau miliyan 100, ya kuke gani?"

AishaYesufu ta ce "Da N20 din da na dage na wahala na samu, ina ganin za su cire N20 na hakura da yi. Na ari wani katin a hannun wasu idan zan yi amfani dashi."

Wata JoyMicah ta ce "Na shiga layin wadanda aka damfara N20. Gaskiya an cuceni kuma an damfareni."

KU KARANTA: Satar 'yan makaranta: Wasu daliban na cigaba da bullowa daga daji, Mai ba Gwamna shawara

fkabudu yace "Oho. Nidai nasan dole sai an ciri kudi. Ka kirga N20 sau yawan 'yan Najeriya."

Wata derra_o ta ce, "Na so duba na layina, amma sai naga sai an cire N20. Shine na fasa yi. Kun dade baku rufe katin nawa ba."

A wani labari na daban, bayan Dino Melaye ya baiwa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan hakuri, akan yadda ya tsaya kai-da-fata wurin ganin sun saukeshi daga mulki, Bala Mohammed ya sara wa Jonathan, har yana kiransa da sadauki.

A ranar Talata, Jonathan yace wasu abokansa da abokan hamayyarsa na siyasa sunyi masa mummunan zato kafin zaben shugaban kasa na 2015 saboda dagewarsa da burinsa na ciyar da kasarnan gaba.

Duk da hakan, yace bai rike kowa a zuciyarsa ba, duk da kushe da zagon kasar da akayita masa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel