Ta'addancin 'Yan Bindiga Ya Ritsa da Sojoji da Mai Juna Biyu a Taraba

Ta'addancin 'Yan Bindiga Ya Ritsa da Sojoji da Mai Juna Biyu a Taraba

  • ’Yan bindiga sun kashe soja, mafarauci da mata mai juna biyu a ƙauyen Sarkin Yamma, kusa da Jeb-Jeb a jihar Taraba
  • Maharan sun kuma jikkata wani soja tare da sace mutane da dama, ciki har da mata da yara, a ƙauyukan Sarkin Yamma da Ruwan Zafi
  • Wani shugaban al’umma ya ce mutane 15 na ci gaba da kasancewa a hannun ’yan bindigar, yayin da ya roƙi gwamnati ta ƙara tsaro a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Taraba - Wasu ’yan bindiga sun kashe soja, mafarauci da wata mata mai juna biyu a ƙauyen Sarkin Yamma, kusa da yankin Jeb-Jeb da ke Ƙaramar Hukumar Karim-Lamido ta Jihar Taraba.

Maharan sun kuma harbi wani soja tare da jikkata shi, sannan suka yi awon gaba da wasu mazauna yankin a daren ranar Talata, 3 ga watan Nuwamban 2026.

Kara karanta wannan

EFCC ta bankado haramtacciyar matatar mai ta 'yan kasar waje cikin daji

'Yan bindiga sun hallaka soja a Taraba
Shugaban rundunar sojojin kasa ta Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa maharan, waɗanda ke ɗauke da manyan makamai, sun kai hare-haren ne kwanaki 11 bayan wani mummunan hari da suka kai garin Binnari.

A harin na Binnari, an bayar da rahoton cewa sama da mutum 60 ne aka kashe, ciki har da mata da yara.

An sace mutane 15 a Ruwan Zafi

Bayan harin Sarkin Yamma, maharan sun kuma shiga ƙauyen Ruwan Zafi, wanda ke kusa da yankin, inda suka yi garkuwa da mutane 15, ciki har da mata da yara.

Wani shugaban al’umma a yankin, Tanko Bobbo Andami, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da yake zantawa da jaridar Daily Trust ta wayar tarho.

Andami ya ce maharan sun shiga ƙauyukan ne a daren Talata, inda suka kashe soja, mafarauci da mata mai juna biyu, sannan suka jikkata wani soja.

Ya bayyana cewa an samu nasarar ceto mutane biyar bayan da sojoji da mafarautan yankin suka yi artabu da maharan.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Mai garkuwa da mutane ya shiga hannu yana kokarin karbar kudin fansa

A cewarsa, musayar wutar ta tilasta wa ’yan bindigar tserewa zuwa cikin daji, inda suka tafi da wasu daga cikin mutanen da suka yi garkuwa da su.

Sai dai Andami ya ce kusan mutane 15 na ci gaba da kasancewa a hannun maharan, lamarin da ya ƙara tsananta matsalar rashin tsaro a Ƙaramar Hukumar Karim-Lamido.

An roƙi gwamnati ta ƙara tsaro

Shugaban al’ummar ya ce sun sha yin kira ga gwamnati da ta ɗauki matakan kare yankin tun kafin hare-haren Binnari da kuma sabon harin da aka kai.

"Kafin hare-haren garin Binnari da wannan sabon lamari, mun yi kira ga gwamnati da ta samar da tsaro a Karim-Lamido kafin ’yan bindiga su mamaye yankin. Ga halin da muka shiga yanzu.” In ji shi.

Ya ƙara da cewa suna sake roƙon gwamnatin Jihar Taraba da Gwamnatin Tarayya da su mayar da hankali na musamman kan yankin.

Andami ya buƙaci hukumomin su samar da isasshen tsaro domin kare al’ummar Ƙaramar Hukumar Karim-Lamido daga hare-haren ’yan bindiga.

Rundunar ’yan sanda ba ta yi magana ba

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar Taraba, ASP Victor Mshelizah, bai amsa kiran wayar da wakilin jaridar ya yi masa domin jin ta bakinsa kan lamarin ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun rutsa 'yan islamiya a jihar Neja an sace dalibai ‘yan mata

Saboda haka, ba a samu ƙarin bayani daga rundunar ’yan sandan jihar kan harin na 'yan bindiga ba.

'Yan bindiga sun kashe soja a Taraba
Taswirar jihar Taraba, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan bindiga sun kashe dan agajin Izalah

A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta yi alhini kan rasuwar ɗaya daga cikin mambobinta, Abubakar Yusuf Sokoto, wanda ya rasu a harin ’yan bindiga a jihar Zamfara.

Marigayin, wanda ke aiki a rundunar ’yan sandan Najeriya, ya rasa ransa ne yayin da wasu ’yan bindiga suka kai wa tawagar jami’an tsaro hari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng