Shehu Idris, Ado Bayero, Lamido da Sarakunan Arewa da suka yi tsawon rai a karagar mulki

Shehu Idris, Ado Bayero, Lamido da Sarakunan Arewa da suka yi tsawon rai a karagar mulki

  • Mun tattaro fitattun Sarakunan kasar Arewa da suka shafe shekara da shekaru suna kan mulki
  • Daga cikin Sarakunan da suka yi tsawon rai akwai su Ado Bayero, da kuma Lamidon Adamawa
  • A cikin shekarar nan ta 2021 ne Sarkin Wukari, Shekarau Angyu Masa Ibi da Mai Sudan suka rasu

Jaridar Message Arewa ta fitar da jerin wasu sarakunan Arewa da aka yi wadanda suka dade suna mulki, sun dauki shekara da shekaru a kan karaga.

Wanda ya rasu a karshe a wannan jeri shi ne Sarkin Wukari, Shekarau Angyu Masa Ibi CFR. Akwai wasu Sarakunan da ba a kawo sunayensu a nan ba.

Ga jerin nan kamar yadda aka kawo su a shafin North Pad:

Kara karanta wannan

Abubuwa 6 da ya kamata a sani game da Marubucin ‘Kulba na barna’ da ya rasu a yau

1. Sarkin Kagoro, Gwamna Awan

Tsohon Sarkin Kagora, Gwamna Awan shi ne Sarkin da ya fi kowa dade a Najeriya da Afrika. Awan ya yi mulki na shekara 63 tun daga 1945 har 2008.

2. Lamidon Adamawa, Aliyu Mustapha Barkindo

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Marigayi Lamidon Adamawa na 11, Aliyu Mustapha Barkindo ya shafe shekaru 57 yana kan mulki. Barkindo ya hau mulki a 1953, ya rasu ne a 2010.

3. Attah na Igala, Aliyu Obaje, CFR

Attah Aliyu Obaje yana cikin Sarakan da suka dade suna kan gadon sarauta. Obaje ya mulki kasar Igala na tsawon shekaru 56 kafin ya rasu a shekara 102.

4. Sarkin Daura, Abdulrahman

Mai Daura, Abdulrahman ya yi mulki tsakanin shekarar 1912 da 1966. Bayan ya yi mulki na shekaru 55, sai jikansa, Mamman Bashar ya karbi mulki.

5. Sarkin Kano, Ado Bayero

Kara karanta wannan

Borno: Dakarun soji sun halaka 'yan ta'adda masu hada bam daga takin zamani

Marigayi Mai martaba Ado Bayero yana cikin shahararrun Sarakunan kasar Hausa. Ado Bayero ya karbi mulki a 1962, ya rasu a 2014 yana da shekara 83.

Shehu Idris, da Ado Bayero
Tsofaffin Sarakunan Kano da Zazzau Hoto: allafrica.com
Asali: UGC

6. Sultan Sadiq Abubakar III

Sarkin Musulmi, Sir Siddiq Abubakar na III ya rike kujerar Sultan daga 1938 zuwa 1988. Shi ne wanda ya fi kowa dadewa a kan karagar Sarkin Musulmi.

7. Sarkin Kagara, Alhaji Salihu Tanko

A shekarar nan Sarkin Kagara, Salihu Tanko ya rasu bayan shekaru 51 yana mulki. Marigayin ya fara ne daga hakimcin Tegina a 1971,kafin ya zama Sarkin Kagara.

7. Sarkin Kontagora, Saidu Namaska

Tsohon Sarkin Sudan, Alhaji Sai’du Namasaki wanda jika ne wajen Shehu Usman Danfodio ya yi shekara 47 yana mulkar kasar Kontagora kafin ya mutu a 2021.

8. Sarkin Zazzau, Shehu Idris

Marigayi Shehu Idris shi ne Sarkin ya fi dadewa a kan mulki a tarihin kasar Hausa. Bayan yazama Sarki a 1975, ya yi shekara 45 kafin ya rasu yana shekara 84.

Kara karanta wannan

Farfesan shari’a mai shekaru sama da 90 ya na cikin wadanda suka zama SAN a 2021

9. Sarkin Wukari, Shekarau Angyu Masa Ibi

A watannin bayan nan ne Shekarau Angyu Masa Ibi Kuvyo II, Aku-Uka na Wukari ya rasu. Aku-Ukan na 27 ya mulki Jukunawan Najeriya har na shekaru 45.

10. Sarkin Lafia, Mustafa Agwai

Mustafa Agwai I wanda ya mulki kasar Lafiya tsakanin 1974 da 2019 ya yi shekaru 43 yana rike da mutanensa. Shi ma ya rasu ne yana mai shekaru 84 a 2019.

11. Sarkin Daura, Muhammadu Bashar of Daura

Masarautar Daura ce kadai ta samu wakilci biyu a jerin da Message Arewa tayi. Shi ma Muhammadu Bashar wanda ya rasu a 2007 ya yi shekara 41 a mulki.

Sarkin Lafiagi ya rasu

Kwanakin baya aka ji cewa Sarkin Lafiagi, Alhaji Saadu Kawu Haliru ya rasu. Rahotanni sun ce basaraken ya rasu ne a wani asibiti da ke babban birnin tarayya, Abuja.

Marigayi Sarkin Lafiagi, Sarki ne mai sanda mai daraja ta ɗaya wanda ya hau mulki a 1975 kuma ya yi bikin cika shekaru 45 kan mulki a ranar 21 ga watan Oktoban 2020.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Shugabannin Ƴan Ta’adda da Ƴan Bindiga Da Aka Kashe Daga Farkon Shekarar 2021 Zuwa Yanzu

Asali: Legit.ng

Online view pixel