Farfesan shari’a mai shekaru sama da 90 ya na cikin wadanda suka zama SAN a 2021

Farfesan shari’a mai shekaru sama da 90 ya na cikin wadanda suka zama SAN a 2021

  • Farfesa Ajagbe Toriola Oyewo ya kai mukamin SAN yana da shekaru 91
  • Dattijon malamin ya kai matakin SAN shekara 60 da fara yin aikin lauya
  • Ajagbe Toriola Oyewo tsohon malamin makaranta ne, kuma ya yi siyasa

Nigeria - Wani Farfesan shari’a, Ajagbe Toriola Oyewo, yana cikin wadanda suka zama sababbin manyan lauyoyi watau SAN a Najeriya a shekarar 2021.

Jaridar The Nigerian Lawyer tace Farfesa Ajagbe Toriola Oyewo mai shekara 91 a Duniya, yana cikin wadanda za a rantsar a matsayin sababbin SAN a bana.

An haifi dattijon lauyan ne a garin Erunmu, jihar Oyo a ranar 11 ga watan Junairu, 1932.

Wani rahoto da aka fitar a ranar Lahadi, 24 ga watan Oktoba, 2021, ya nuna cewa Farfesa Ajagbe Toriola Oyewo yana da sarautar gargajiya a Ibadan, jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Mourinho ya sha mummunan kashi a hannun karamin kulob, an dirka masa kwallaye 6

Baya ga sarauta, Ajagbe Oyewo ya taba shiga harkar siyasa, har ya zama ‘dan majalisa mai wakiltar mazabar Lagelu ta Kudu a majalisar wakilai na tarayya.

Farfesan shari’a
Ajagbe Toriola Oyewo SAN
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Karatun Ajagbe Toriola Oyewo

Oyewo yayi digirin farko na LL.B a Landan a 1960, ya yi digirgir na MPA 1973, da digirin M. Phil a 1983, a 1985 ya kammala karatun digirinsa na uku watau PhD.

A shekarar 1962 ya fara aikin lauya, kuma yana cikin kungiyar lauyoyin Lincoln’s Inn da ke Landan. Oyewo ya kware kan sha’anin kananan hukumomi.

Sababbin SANs na shekarar 2021.

Farfesan yana tare da wasu malaman makaranta a rukunin sabon shiga mukamin SAN a 2021.

A wannan karo, sauran malaman makarantar da suka samu karin matsayi zuwa matakin SAN a harkar lauyanci sun hada da wasu takwarorinsa, Farfesa goma.

Farfesoshin sune; Bankole Akintoye Sodipo, Christian Chizundu Wigwe, Ajagbe Toriola Oyewo, Rasheed Jimoh Ijaodola, da kuma Oluyinka Osayame Omorogbe.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Shugaban NHRC da sauran manyan lauyoyi 71 da suka samu girmamawa ta SAN

Sai Edoba Bright Omoregie, Abiola Olaitan Sanni, Dr. Josephine Aladi A. Agbonika, da Dr. Ibrahim Abdullahi. Za a rantsar da dukkaninsu a Disamban shekarar nan.

Dalilin da ya sa na bar Mauludi - Ibrahim Disina

Kwanakin baya aka ji babban malamin addinin musulunci, Dr. Ibrahim Omar Adama Disina yana cewa yana cikin ‘Yan Mauludi kafin ya hadu da Malaman Izala.

Wannan malamin da yake bin akidar Salafiyyah ya rabu da sha’anin Mauludi bayan ya yi karatu. Shehin ya bayyana wannan ne da yake magana a shafin Facebook.

Asali: Legit.ng

Online view pixel