Sarki mai daraja ta ɗaya a Arewa ya rasu bayan shekaru 45 kan karagar mulki

Sarki mai daraja ta ɗaya a Arewa ya rasu bayan shekaru 45 kan karagar mulki

  • Alhaji Sa'adu Kawu Haliru, sarkin Lafiagi a jihar Kwara ya riga mu gidan gaskiya
  • Sarkin ya rasu ne a ranar Alhamis 9 ga watan Yuli a wani asibiti da ke birnin tarayya Abuja
  • Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya tabbatar da rasuwar Sarkin tare da yin ta'aziyya

Sarkin Lafiagi, Alhaji Saadu Kawu Haliru ya riga mu gidan gaskiya kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Rahotanni sun ce basaraken ya rasu ne a wani asibiti a Abuja misalin ƙarfe 6 na yammacin ranar Alhamis.

Sarki mai daraja ta ɗaya a Arewa ya rasu bayan shekaru 45 kan karagar mulki
Sarki mai daraja ta ɗaya a Arewa ya rasu bayan shekaru 45 kan karagar mulki. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Kano: Ɗalibi ya cinnawa kansa wuta saboda bai samu kuɗin biyan jarrabawar NECO ba

Wata majiya ta shaidawa Daily Trust cewa za a kai gawarsa jihar Kwara a ranar Juma'a zuwa Lafiagi, ƙaramar hukumar Edu inda za a yi masa jana'iza bisa koyarwar addinin musulunci.

Marigayi Sarkin Lafiagi, sarki ne mai sanda mai daraja ta ɗaya wanda ya hau mulki a 1975 kuma ya yi bikin cika shekaru 45 kan mulki a ranar 21 ga watan Oktoban 2020.

Da ya ke tabbatar da rasuwar, Ndegi na Lafiagi, Alhaji Ahmed Kaiama, ɗaya daga cikin masu zaɓen sarki ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga ƙasar Nupe.

Marigayin ne shugaban majalisar gidan Radio Kwara.

Gwamnan Kwara ya yi ta'aziyyar rasuwar Sarkin

A sakonsa na ta'aziyya, Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ya bayyana Marigayin Sarkin a matsayin mai kira ga zaman lafiya da hadin kai kuma rasuwarsa ya kawo ƙarshen wani zamani mai daraja.

KU KARANTA: Hotunan mataimakin kwamishinan Ƴan Sanda na bogi da aka kama cikin otel a Kano

Abdulrazaq ya ce:

"Sarkin mai daraja ta ɗaya mutum ne mai baiwar basira ta sarauta, tausayi da zaman lafiya. Ya kasance yana kira ga zaman lafiya da haɗin kai duk da banbancin da ke tsakanin mutane, hakan yasa aka samu gagarumin cigaba a zamanin sarautarsa."
"Rasuwar mai martaba ta kawo karshen wani muhimmin shafi a tarihi, duba da cewa shi ya jagoranci farfaɗo da al'adu da inganta rayuwar al'ummarsa tsawon shekaru 45 da suka shuɗe."

Gwamnatin Katsina za ta wajabtawa kowanne baligi harajin N2000, shanu kuma N500 matsayin Jangali

Gwamnatin jihar Katsina za ta fara karbar harajin Jangali na N500 akan kowacce saniya da ke jihar duk shekara kamar yadda News Wire ta ruwaito.

The Cable ta ruwaito cewa gwamnatin jihar ta gabatar da tsarin amsar kudin bunkasa jihar da kuma jangalin shanu.

Alhaji Faruk Jobe, kwamishinan kasafi da tattalin jihar ne ya bayyana hakan a ranar Laraba bayan wani taro na masu ruwa da tsakin jihar wanda gwamna Aminu Masari ya shirya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel