Abubuwa 6 da ya kamata a sani game da Marubucin ‘Kulba na barna’ da ya rasu a yau

Abubuwa 6 da ya kamata a sani game da Marubucin ‘Kulba na barna’ da ya rasu a yau

  • A asuban yau ne, Juma’a, 29 ga watan Oktoba, 2021, Alhaji Umaru Danjuma Katsina ya bar Duniya
  • Umaru Danjuma Katsina ya yi suna saboda wasu rubuce-rubucen da ya yi tun yana karamin yaro
  • Marigayin ya rubuta kulba na barna, yana 'dan makaranta a shekara 19 , kuma yace labarin ya faru

Katsina - A ranar Juma’ar nan, 29 ga watan Oktoba, 2021, aka samu labarin babban marubuci kuma dan wasan kasar Hausa, Umaru Danjuma Katsina, ya rasu.

Alhaji Umaru Danjuma Katsina, ya bar Duniya yana da shekaru 71 da watanni shida da kwana 19.

Mutane da dama sun san marigayin dalilin littafinsa da ya rubuta mai suna Kulba na barna. Bayan nan ya kara tashe a shirin wasan kwaikwayon Kasagi (na Halima).

1. Wanene Umaru Danjuma Katsina?

Legit.ng Hausa ta tsakuro takaitaccen tarihinsa kamar yadda ake bada a wajen bikin HIBAF.

Read also

Borno: Dakarun soji sun halaka 'yan ta'adda masu hada bam daga takin zamani

An haifi Kasagi na Halima a Afrilun 1950 a unguwar Kofar Soro, Katsina. Sunan mahaifinsa Muhammadu Danjuma, sunan mahaifiyarsa kuma Hajara Lonso.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. Karatun boko da fara aiki

A shekarar 1966 ne Marigayin ya shiga makarantar Firamare a Katsina, ya gama a 1972. Daga nan ya fara karatun sakandarensa a GSSS Katsina daga 1972 zuwa 1975.

Tsakanin 1975 da 1980, Umaru Danjuma Katsina yana makarantar koyar da fim da ke Landan, ya yi Difloma da babbar Difloma a harkar shirya wasan kwaikwayo.

Ummaru Danjuma Katsina
Marigayi Ummaru Danjuma Katsina a Arewa House Hoto: Open Arts / HIBAF21
Source: Facebook

Tun a 1972 Danjuma Katsina ya soma aiki a matsayin karamin jami’in al’adu a rusasshiyar jihar Arewa ta tsakiya. Daga baya ya koma ABU Zaria a shekarar 1978.

A 1986 ne Danjuma ya samu karin matsayi, ya kai matakin malamin al’adu a jami’ar. Daga nan ya koma aiki a karkashin gwamnatin Katsina, har ya yi ritaya a 1991.

Read also

Yan sanda sun damke wani mutumi kan laifin turawa matar aure sakon "Inakwana Baby"

A shekarar nan aka sake ba Marigayin aiki a matsayin cibiyar tarihi da al’adu na jihar Katsina.

3. Littatafan Umaru Danjuma:

Kulba na barna I da II

Ai ga irinta nan

Bakin bature da

Agony of justtice

4. Wasu wasan kwaikwayon da ya shirya:

Goggo mai gyada

Kishiya

‘Ya ‘yan zamani

Muna ji muna gani

Kowa da zamaninsa

5. Fitowa a wasan kwaikwayo (fim):

Tauraron ya fito a shirin fim da aka yi irinsu:

Second circle

Magana jari ce

Kasagi

6. Ganin Kasagi na karshe da aka yi

A ranar 22 ga watan Oktoba, 2021, aka karrama Umaru Danjuma Katsina a wajen bajakolin Hausa Int’l Books and Arts Festival da aka shirya a garin Kaduna.

Mai martaba Dan Isan Zazzau, ne ya ba shi wannan kyauta a madadin Sarkin Zazzau, Ahmad Bamalli.

Bikin HIBAF21 da aka shirya a Kaduna

A baya kun ji cewa an shirya bikin bajakolin fasahohi da littatafan Hausawa da aka yi a Kaduna. Cikin wadanda suka ba taron armashi har da uwargidar jihar Kaduna.

Read also

A karon farko, an samu kungiyar da ta yi gagarumin biki domin bunkasa harshen Hausa

Kun ji cewa marubutan Arewacin Najeriya da ‘yan wasan kwaikwayo da taurari sun halarci taron. A wajen bikin ne aka ba Danjuma Katsina lambar girmamawa.

Source: Legit.ng

Online view pixel