Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari Ya dawo daga Kasar Saudiyya

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari Ya dawo daga Kasar Saudiyya

  • Bayan taron zuba jari da gudanar da Ibadah a kasa mai tsarki, shugaban kasa ya iso gida Najeriya
  • Buhari ya samu tarba daga wajen manyan jami'an gwamnati cikinsu har da Sifeto Janar na yan sanda
  • Buhari ya yiwa Najeriya addu'a a raudan Manzon Allah a Madina inda ya yadi zango

Abuja - Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya dira a birnin tarayya Abuja da yammacin Juma'a, 29 ga Oktoba, bayan tafiyar kwana biyar da yayi Kasar Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ta ruwaito cewa Shugaba Buhari da mukarrabansa sun tashi daga filin jirgin Sarki AbdulAzizi dake Jiddah misalin karfe 15:45.

A kwanaki biyar da yayi a Saudiyya, Buhari ya ziyarci Riyadh, Makkah da Madina.

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari Ya dawo daga Kasar Saudiyya
Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari Ya dawo daga Kasar Saudiyya
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Bidiyon hamshakan yan kasuwa sanye da kayan harami cikin jirgi ya bayyana

Buhari a Masallacin Annabi, ya kwarara wa Najeriya addu'o'in zaman lafiya

A ranar Laraba, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karasa Birnin Makkah da ke kasar Saudiya domin yin Umrah.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, a wata takarda da ya fitar, ya ce Buhari da tawagarsa sun yi wa Najeriya da jama'ar ta fatan samun zaman lafiya da tsaro.

Kamar yadda Shehu ya bayyana, ya ce addu'o'in har da na fatan habakar tattalin arziki bayan annobar korona domin karuwar kasar nan da jama'ar ta.

Ya ce mataimakin gwamnan yankin, Yarima Sa'ud Al-Faisal ne ya karba shugaban kasar a filin sauka da tashin jiragen sama na Yarima Muhammad Abdulaziz da ke Madina.

Sun kwashe tsawon lokaci a cikin Masjid Annabawi inda suka dinga addu'o'i da karatun Al-Qur'ani mai girma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel