Deliget 3600 sun dira Abuja yayinda kotu ke shirin raba gardama tsakanin Uche Secondus da PDP

Deliget 3600 sun dira Abuja yayinda kotu ke shirin raba gardama tsakanin Uche Secondus da PDP

  • Yayinda kotu ke shirya yanke hukunci, wakilan PDP daga jihohin Najeriya 36 sun fara dira birnin tarayya Abuja
  • Jam'iyyar PDP ta shirya yin taron gangaminta ne a ranar Asabar da Lahadi don zaben sabbin shugabanni
  • Amma da alamun taron ba zai yiwu ba saboda tsohon shugaba Uche Secondus ya shigar da jam'iyyar kotu

Abuja - Deliget sun fara dira birnin tarayya Abuja domin musharaka a taron gangamin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP da aka shirya yi ranar Asabar, 30 ga Oktoba.

Wannan na faruwa duk da cewa har yanzu babu tabbacin taron gangamin zai yiwu saboda rikicin dage gudana a kotu tsakanin tsohon shugaban uwar jam'iyyar, Uche Secondus da jam'iyyar.

Punch ta ruwaito cewa tuni an fara yiwa farfajiyar Eagle Square kwalliya da tutotin PDP, inda taron zai gudana.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Ban gamsu da ayyukan da Ganduje ya yi a Kano ba, In ji Kwankwaso

Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Gombe, Manjo Janar Mamman Kwasjebe (mai murabus) ya bayyanawa Punch cewa:

"Tuni ina Abuja; wannan taron gangamin za'a yi shi,"

Hakazalika shugaban PDP na jihar Cross River, Venatius Ikem, ya bayyana cewa yana da tabbacin wannan taro zai yiwu kamar yadda aka shirya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace tuni yana Abuja tare da sauran deliget da suka dira Abuja daga fadin tarayya.

Deliget na PDP 3600 sun dira Abuja
Deliget 3600 sun dira Abuja yayinda kotu ke shirin raba gardama tsakanin Uche Secondus da PDP
Asali: Depositphotos

Kotun daukaka kara zata raba gardama tsakanin Uche Secondus da PDP ranar Juma'a

Kotun daukaka kara dake zaune a birnin Fatakwal, jihar Rivers zata yanke hukunci kan karar da tsohon shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, Uche Secondus, ya shigar kan jam'iyyarsa.

Kwamitin Alkalan uku karkashin jagoranicn Justice Haruna Tsammani, sun jingine yanke hukunci zuwa ranar Juma'a bayan sauraron jawabin lauyar Secondus, Tayo Oyetibo da lauyoyin PDP, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara zata raba gardama tsakanin Uche Secondus da PDP ranar Juma'a

Uche Secondus ya shigar da PDP kotu ne bayan saukesa da akayi kan kujerarsa karfi da yaji

Secondus bai yi mana adalci ba idan ya rusa PDP, Shugaban kwamitin dattawan jam'iyyar Walid Jibrin

Shugaban kwamitin amintattun jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Walid Jibril, ya yi kira ga dakataccen shugaban jam'iyyar Walid Jibrin kada ya kawo hargitsi cikin jam'iyyar.

Alhaji Walid ya bayyana hakan ne yayin jawabi a shirin Sunrise Daily, na ChannelsTV ranar Laraba, TheCable ta bibiya.

A cewarsa, uwar jam'iyyar ta yanke shawara ta karshe kuma lallai za'ayi taron gangami ranar da aka shirya.

Yace ba zai kyautatu ga Secondus, wanda yana cikin iyayen jam'iyyar PDP ya dagula musu lissafi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel