Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara zata raba gardama tsakanin Uche Secondus da PDP ranar Juma'a

Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara zata raba gardama tsakanin Uche Secondus da PDP ranar Juma'a

  • Ana saura kwana biyu taron gangamin jam'iyyar PDP, Kotu ta bayyana ranar da zata yanke hukuncinta
  • Alkalai uku dake kan lamarin a zaman kotun ranar Alhamis sun saurari hujjojin dukkan bangarorin biyu
  • Uche Secondus ya lashi takobin cewa ba zai yarda a gudanar da wannan zabe

Rivers - Kotun daukaka kara dake zaune a birnin Fatakwal, jihar Rivers zata yanke hukunci kan karar da tsohon shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, Uche Secondus, ya shigar kan jam'iyyarsa.

Kwamitin Alkalan uku karkashin jagoranicn Justice Haruna Tsammani, sun jingine yanke hukunci zuwa ranar Juma'a bayan sauraron jawabin lauyar Secondus, Tayo Oyetibo da lauyoyin PDP, rahoton Punch.

Uche Secondus ya shigar da PDP kotu ne bayan saukesa da akayi kan kujerarsa karfi da yaji

Kara karanta wannan

Yan sanda sun damke wani mutumi kan laifin turawa matar aure sakon "Inakwana Baby"

Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara ta yi watsi karar Uche Secondus, tace ayi taron PDP lafiya
Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara ta yi watsi karar Uche Secondus, tace ayi taron PDP lafiya Hoto: OfficialPDP

Secondus bai yi mana adalci ba idan ya rusa PDP, Shugaban kwamitin dattawan jam'iyyar Walid Jibrin

Shugaban kwamitin amintattun jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Walid Jibril, ya yi kira ga dakataccen shugaban jam'iyyar Walid Jibrin kada ya kawo hargitsi cikin jam'iyyar.

Alhaji Walid ya bayyana hakan ne yayin jawabi a shirin Sunrise Daily, na ChannelsTV ranar Laraba, TheCable ta bibiya.

A cewarsa, uwar jam'iyyar ta yanke shawara ta karshe kuma lallai za'ayi taron gangami ranar da aka shirya.

Yace ba zai kyautatu ga Secondus, wanda yana cikin iyayen jam'iyyar PDP ya dagula musu lissafi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel