Garkuwa da mutane: NSCDC ta tura tawagar mata ta musamman domin tsaron makarantu a Adamawa

Garkuwa da mutane: NSCDC ta tura tawagar mata ta musamman domin tsaron makarantu a Adamawa

  • Hukumar NSCDC ta tura tawagar tsaro na Jami’ai mata domin tsaron makarantu a fadin jihar Adamawa
  • Shugaban NSCDC a jihar, Usman Waksha ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Alhamis
  • Ya ce hakan na daga cikin shirin gwamnatin tarayya na samar da tsaro a makarantu

Jihar Adamawa - Hukumar tsaro ta NSCDC ta tura runduna ta musamman ta mata zuwa makarantu a fadin kananan hukumomi 21 da ke jihar Adamawa.

Kwamandan NSCDC a jihar, Usman Waksha ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Alhamis a garin Yola, babbar birnin jihar, Channels TV ta rahoto.

Garkuwa da mutane: NSCDC ta tura tawagar mata ta musamman domin tsaron makarantu a Adamawa
Garkuwa da mutane: NSCDC ta tura tawagar mata ta musamman domin tsaron makarantu a Adamawa Hoto: NSCDC
Asali: Facebook

A cewarsa, tura Jami’an da aka yi ya yi daidai da shirin gwamnatin tarayya na samar da isasshen tsaro ga makarantu da kuma kokarin babban kwamandan NSCDC na magance kalubalen tsaro a makarantu a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Matasa sama da 172 sun haukace a jihar Zamfara

Ya ce:

“A yau, muna kaddamar da runduna ta musamman da shirin samar da tsaro a makaranta. Za a tura motoci da jami’anmu da suka samu horo na musamman zuwa wurare masu muhimmanci a jihar.
“Za kuma a tura Jami’ai zuwa makarantu. Shiri ne da zai ci gaba, muna fatan kaiwa ga dukkan makarantu.”

Kwamandan ya kuma yi alkawarin cewa hukumar za ta ci gaba da yin iya bakin kokarinta sannan ya roki mazauna jihar da su ba Jami’an hadin kai domin tsaron makarantu.

Kimanin jami’an NSCDC 60 aka tura makarantun kwana da na jeka ka dawo a jihar Adamawa domin tsaronsu da kuma wanzar da zaman lafiya a cikinsu.

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce sama da yara miliyan 12 na Najeriya, wanda mata suka fi yawa a ciki sun tsorata kuma suna tsoron zuwa makaranta sakamakon farmakin da 'yan ta'adda ke kai wa makarantu.

Kara karanta wannan

Satar 'yan makaranta: Sama da dalibai 12m sun firgita, su na tsoron zuwa makaranta, Buhari

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya sanar da hakan a Abuja a ranar Talata yayin kaddamar da taro kashi na hudu na International Conference on Safe Schools Declaration.

Ya ce satar yaran makaranta, karuwar al'amuran ta'addanci da kuma dukkan matsalolin rashin tsaro sun taka rawar gani wurin kara yawan yaran da basu zuwa makaranta, Daily Trust ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel