Satar 'yan makaranta: Sama da dalibai 12m sun firgita, su na tsoron zuwa makaranta, Buhari

Satar 'yan makaranta: Sama da dalibai 12m sun firgita, su na tsoron zuwa makaranta, Buhari

  • Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa sama da yara 12 miliyan ne a Najeriya ke cike da firgici tare da tsoron zuwa makaranta
  • Shugaban kasan ya ce satar yaran makaranta da 'yan ta'adda ke yi ta taka rawa wurin kara yawan yaran da basu zuwa makaranta a Najeriya
  • Ta bakin Gambari wanda ya wakilci Buhari, ya ce gwamnati ta mayar da hankali wurin inganta tsaro a makarantun kasar nan

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce sama da yara miliyan 12 na Najeriya, wanda mata suka fi yawa a ciki sun tsorata kuma suna tsoron zuwa makaranta sakamakon farmakin da 'yan ta'adda ke kai wa makarantu.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya sanar da hakan a Abuja a ranar Talata yayin kaddamar da taro kashi na hudu na International Conference on Safe Schools Declaration.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga: Sarkin Birnin Gwari ya bayyana alherin da katse hanyoyin sadarwa ya jawo

Satar 'yan makaranta: Sama da dalibai 12m sun firgita, su na tsoron zuwa makaranta, Buhari
Satar 'yan makaranta: Sama da dalibai 12m sun firgita, su na tsoron zuwa makaranta, Buhari. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce satar yaran makaranta, karuwar al'amuran ta'addanci da kuma dukkan matsalolin rashin tsaro sun taka rawar gani wurin kara yawan yaran da basu zuwa makaranta, Daily Trust ta wallafa.

Buhari, wanda ya samu wakilcin shugaban ma'aikatan fadarsa, Ibrahim Gambari, ya ce 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da 'yan ta'adda suna kutsawa makarantu a duk lokacin da suka so domin sace dalibai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga cikin wuraren da suka shiga tare da sace yara akwai: Chibok, Dapchi, Buni Yadi, Afaka, Kagora, da Jangebe a jihohin Borno, Yobe, Kaduna, Niger da Zamfara.

“Abun takaici ne idan aka ga ko bayan sakin daliban, firgicin lamarin ya na dadewa a zuciyoyinsu. Hakan yasa mu ke kokarin tsara yadda za mu fara horar da malaman taimako a fannin hankali," yace.
Buhari ya ce: "Gaskiya akwai matukar wahala kula da kalubalen tsaro da kuma abubuwan da suke haifarwa. Duk da haka, fatan shawo kan matsalar har yau akwai shi.

Kara karanta wannan

Daga karshe, shugaba Buhari ya gano dalilai uku da suka jawo tabarbarewar tsaro

"Mun jajirce kuma mun dage wurin tabbatar da inganta tsaron makarantu da wadanda ke zuwa."

Tun farko, ministan ilimi, Adamu Adamu, ya ce wannan ne karon farko da aka taba shirya irin wannan taron na ilimi a nahiyar Afrika.

Buhari: Ba zan huta ba har sai na tabbatar Najeriya ba ta fama da kalubalen tsaro

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa mulkinsa ba zai huta ba har sai kalubalen tsaron da Najeriya ke fuskanta a yanzu ta kawo karshe, Daily Nigerian ta ruwaito.

Buhari, wanda ya samu wakailcin ministan kimiyya da fasaha, Dr Ogbonayan Onu, ya sanar da haka ne a yayin gabatar da wani littafi mai suna "Standing Strong" wanda tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani ya rubuta a Abuja.

"Muna cigaba da duba hanyoyi da tsarikan cigaba da nakasa dukkan wani karfin 'yan ta'adda a kasar nan," yace.

Kara karanta wannan

Na'Abba: Buhari ya gaza shawo kan matsalolin Najeriya ne saboda ba ya neman shawara

Asali: Legit.ng

Online view pixel