Sabon hari: 'Yan bindiga sun hari ofishin 'yan sanda, sun kashe 3, an hallaka dan bindiga 1

Sabon hari: 'Yan bindiga sun hari ofishin 'yan sanda, sun kashe 3, an hallaka dan bindiga 1

  • Rahotanni sun bayyana cewa, an hari ofishin 'yan sanda a jihar Ebonyi a yankin kudu maso gabas
  • Akalla 'yan sanda uku ne suka rasa rayukansu, yayin da aka hallaka daya daga cikin 'yan bindigan
  • Ana ci gaba da bincike don gano wadanda suka kai hari, duk da ana zargin IPOB da irin wadannan hare-hare

Ebonyi - The Nation ta ruwaito cewa, an harbe jami’ai uku a cikin ofishin ‘yan sanda da ke Unwana, karamar hukumar Afikpo ta Arewa a jihar Ebonyi.

Wata majiya ta shaida wa Daily Trust cewa jami’an da suka mutu akwai kwanstabul da sifetoci biyu.

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun kai hari ofishin 'yan sanda, sun hallaka jami'ai
'Yan sandan Najeriya | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Wani mazaunin Uwana, wanda bai so a ambaci sunansa ba, ya ce 'yan bindigar sun rufe fuska.

Ya ce an kashe daya daga cikin maharan yayin harin, wanda ya faru da sanyin safiyar Lahadi 24 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

Ya ce:

“Sun kashe 'yan sanda 3; kwanstabul daya da sifetoci biyu kuma 'yan sandan sun kashe daya daga cikin 'yan bindigan.
“Babu wanda ya san su waye 'yan bindigar amma an kai gawar jami’an da aka kashe zuwa dakin ajiye gawa.
“Lamarin ya faru da misalin karfe biyu na safe; babu wanda zai iya gane hanyar da 'yan bindigar suka fito. Abin da kawai muka ji shi ne harbe-harbe na kusan mintuna 10. A halin yanzu, babu wani bayani da za a sani ko sun lalata ko sun sace wani abu daga ofishin 'yan sanda.

“Mutanen sun rufe fuska, amma wanda aka kashen jami’an 'yan sanda sun bude fuskarsa don tabbatar da ko waye shi. Dan bindigan da ya mutu yana daure da jajayen kaya a kugunsa.”

Kara karanta wannan

'Yan Boko Haram sun kai sabon hari Yobe, sun sha ruwan wuta a hannun sojojin Najeriya

Da aka tuntubi kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Aliyu Garba, bai musanta ba kuma bai tabbatar da rahoton ba.

Ba wannan ne karo na farko da ake kai hari ofishin 'yan sanda ba a yankin, an sha rusawa da kone ofishoshin 'yan sanda.

An zargi IPOB da daukar nauyin da kai hare-haren irin wadannnanm amma sun sha musanta hakan.

Rikici ya barke bayan sojoji sun bindige 'yan kungiyar awaren IPOB har 5

A wani labarin, Jaridar Daily Sun ta rahoto cewa, an samu tashin hankali a Arochukwu ta jihar Abia a ranar Alhamis 21 ga watan Oktoba yayin da jami'an tsaro ke fafatawa da 'yan kungiyar awaren IPOB a yankin.

Wani rahoto da ba a tabbatar da shi ba ya nuna cewa mutane hudu da ake zargi 'yan kungiyar IPOB ne ana fargabar an kashe su a yayin fafatawar.

Duk da cewa har yanzu ba a tabbatar da abin da ya jawo harbe-harben ba, wata majiya ta yankin ta ce nan take da yankin ya samu labarin kawo shugaban IPOB Nnamdi Kanu kotu a Abuja don fuskantar shari'a, wasu mambobin IPOB sun hau kan tituna.

Kara karanta wannan

Tsananin kishi ya sa saurayi ture budurwarsa har lahira a Bauchi

Asali: Legit.ng

Online view pixel