Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun fasa gidan yari a jihar Oyo, Sun saki fursunoni duk

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun fasa gidan yari a jihar Oyo, Sun saki fursunoni duk

  • Wasu miyagun yan bindiga sun bi tsakar dare sun ɓarke gidan gyaran hali a jihar Oyo, inda suka saki baki ɗaya fursunoni
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun yi amfani da manyan makamai wajen tilasta wa jami'ai tserewa, kuma su samu damar shiga
  • A halin yanzun hukumomin tsaro sun shirya jami'ai domin taimakawa jami'an tsaron gidan gyaran hali wajen gano maharan da fursunoni

Oyo - Jaridar Vanguard ta rahoto cewa wasu tsagerun yan bindiga sun kai hari gidan yarin dake Abolongo, a jihar Oyo ranar Jumu'a da daddare.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kutsa cikin gidan yarin, sannan suka saki dukkan fursunonin dake ciki.

Miyagun yan bindigan sun fasa gidan yari ne da tsakar dare, inda suka yi amfani da gurneti wajen tilasta samun damar shiga harabar gidan gyaran halin.

Read also

Matsalar tsaro: Miyagun yan bindiga sun ƙone fadar basaraken gargajiya a Najeriya

Gidan gyaran hali
Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun fasa gidan yari a jihar Oyo, Sun saki fursunoni duk Hoto: guardian.ng
Source: UGC

Harin ya jefa gidan gyaran halin cikin mawuyacin hali, yayin da masu gadin wurin suka watse domin neman hanyar tseratar da rayuwarsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hukumar NCS ta tabbatar da harin

Kakakin hukumar tsaron gidan gyaran hali (NCS) reshen jihar Oyo, Olanrewaju Anjorin, ya tabbatar da kai harin.

Dailytrust ta ruwaito kakakin yace:

"Mun tabbatar da cewa an kai hari, kuma a halin yanzu shugaban NCS na jiha da sauran manyan jami'ai suna nazari kan matakin da za'a ɗauka."
"Amma ina mai tabbatar muku da cewa miyagun yan bindiga sun kai hari gidan gyaran hali."

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Zuwa yanzu da muke kawo muku wanna rahoton, tuni sauran hukumomin tsaro suka shirya taimakawa jami'an gidan gyaran hali kan lamarin.

A halin yanzun jami'an tsaro sun kaddamar da bincike, sannan sun bazama nemo maharan da kuma kamo fursunonin da aka kubutar.

Read also

Da duminsa: Yan bindiga sun sake kai hari ofishin yan sanda, sun saki fursunoni

A wani labarin na daban kuma shugaba Buhari ya umarci hafsoshin tsaro komai riɓtsi su tabbatar da an yi zaɓen gwamnan Anambra

Buhari yace duk matakin da ya kamata a ɗauka ya amince a ɗauka domin tabbatar da an baiwa mutane tsaro sun zaɓi shugabannin su.

Ya bada wannan umarnin ne ya yin taron tsaro da ya gudana a fadarsa dake babban birnin tarayya Abuja.

Source: Legit.ng

Online view pixel