Jarumin matukin jirgin kasa, Ziya’u Yusuf, da ya tuka fasinjoji lokacin yan bindiga suka kai hari

Jarumin matukin jirgin kasa, Ziya’u Yusuf, da ya tuka fasinjoji lokacin yan bindiga suka kai hari

  • Yan bindiga sun sanya Bam a layin dogon Abuja-Kaduna ranar Alhamis
  • Babu wanda ya ji rauni kuma dukkan fasinjoji sun tsira
  • Matuki, Ziya'u Yusuf ne matukin da ya nuna jarunta lokacin wannan hadari

Jarumin matukin jirgin kasa, Ziya’u Yusuf shine wanda ke tuka jirgin Kaduna zuwa Abuja lokacin da yan bindiga suka shuka Bam kuma suka budewa jirgin kasar wuta.

Ziya’u Yusuf bai tsaya ba har sai lokacin da ya tabbatar da fasinjojin na cikin tsaro.

An haifi Yusuf a 1988 kuma ya yi karatun Difloma a ilmin Injiniyanci a kwalejin fasahar Abubakar Tatari Ali Polytechnic, Bauchi.

Ya fara aiki da hukumar jiragen kasan Najeriya ne a 2013.

Wani abokin aikinsa wanda yayi hira da DailyNigeria ya bayyana cewa lokacin da jirgin ya taka Bam daidai misalin karfe 7:56 na dare, Yusuf ya umurci abokan aikinsa su kwanta a kasa yayinda yake cigaba da tuka jirgin.

Read also

Da duminsa: Bayan harin yan ta'adda, jirgin kasan Abuja/Kaduna zai koma aiki ranar Asabar

Yace:

"Sashen masu tukin jirgi ne suka fuskanci harsasai. Da farko matukan sun yi tunanin wasu yara ne masu jifan jirgin, amma sun hawa kan dutsuna biyu Bam ya tashi."
"Jirgin ya tashi sama amma kuma ya sauko kan hanya. Bam na tashi aka fara harbin bindiga. Amma Ziya'u bai daina jan jirgin ba har sai da mai ya kare ciki."

Jarumin matukin jirgin kasa, Ziya’u Yusuf, da ya tuka fasinjoji lokacin yan bindiga suka kai hari
Jarumin matukin jirgin kasa, Ziya’u Yusuf, da ya tuka fasinjoji lokacin yan bindiga suka kai hari Hoto: DailyNigerian
Source: Facebook

Yan ta'addan ISWAP da Ansaru ne suka sanya bam a layin dogon Abuja zuwa Kaduna

Yan ta'addan kungiyar ta'addancci ta ISWAP tare da Ansaru ne suke da alhakin lalata layin dogon Abuja zuwa Kaduna, majiyoyi masu karfi na tsaro suka tabbatar wa da Daily Trust a ranar Alhamis.

Karaikainar jiragen kasa daga Abuja zuwa Kaduna ta gurgunta na wucin-gadi daga daren Laraba zuwa Alhamis bayan an gano cewa 'yan ta'adda sun sanya bam tare da tashin wani sashi na layin dogon.

Read also

Sai mun hada kai ne za mu iya cin galaba a kan miyagu – APC kan harin jirgin kasa

Miyagun sun koma da sa'o'in farko na ranar Alhamis inda suka sake lalata wani sashi na layin dogon, lamarin da yasa hukumar jiragen kasa ta Najeriya ta dakatar da ayyukan ta.

Wani babban jami'in tsaro ya tabbatar wa da Daily Trust cewa, a cikin kwanakin da suka gabata, jami'an tsaro sun tare da halaka wasu 'yan ta'addan da suka yi yunkurin saka bam a gadoji da layikan dogo a Kaduna.

Source: Legit

Online view pixel