Shugaba Buhari zai kaddamar da e-Naira ranar Litinin kafin ya tafi Saudiyya

Shugaba Buhari zai kaddamar da e-Naira ranar Litinin kafin ya tafi Saudiyya

  • eNaira wani sabon kudin Najeriya ne da Bankin CBN zai fitar don amfanin yan Najeriya
  • A baya bankin ya dage taron kaddamar da eNaira ranar 1 ga Oktoba saboda murnar ranar yancin kai
  • CBN yace yan Najeriya zasu iya amfani da wannan Naira kamar yadda suke amfani da na takarda

Shugaba Muhammadu Buhari zai kaddamar da tsarin gwajin kudin intanet da aka yiwa lakabi da eNaira Abubuwan da ya kamata ku sani tsakanin kudin intanet na Najeriya a fadar Aso Villa, ranar Litinin, 26 ga Oktoba, 2021.

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana hakan a jawabin da Diraktan labarai na bankin, Osita Nwanisobi, ya saki ranar Asabar.

A ranar 1 ga Oktoba, CBN ya shirya kaddamar da eNaira amma aka dakatar saboda wasu matsaloli.

Read also

Dama ta samu: Buhari zai ba masu digiri bashin miliyoyi saboda rage zaman banza

Jawabin yace:

"Biyo bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki wanda ya hada da bakunan Najeriya, masana tasarrufin kudin zamani, yan kasuwa da wasu yan Najeriya, za'a fara amfani da kudin da CBN ta tsara daga ranar Litinin, 25 ga Oktoba, 2021."
"CBN shirya take da tabbatar da cewa kowa ya samu eNaira kamar yadda ake samun kudin takarda."

Da duminsa: Shugaba Buhari zai kaddamar E-Naira ranar Litnin
Da duminsa: Shugaba Buhari zai kaddamar E-Naira ranar Litnin Source: @centralbankofNigeia
Source: Facebook

Abubuwan da ya kamata ku sani game da kudin intanet na Najeriya

CBDC wakilci ne na tsarin kudaden intanet masu cikakken iko da ake samar da su kamar yadda Babban Banki ke samar da kudi gama-gari.

Alhakin kai tsaye ne na Babban Banki ke samar dashi. Ba ana nufin maye gurbin tsabar kudi da tsarin ajiyar banki bane, ana nufin su yi aiki kunnen doki a matsayin karin nau'in hanyar biyan kudi da karba.

Read also

Da duminsa: Bayan harin yan ta'adda, jirgin kasan Abuja/Kaduna zai koma aiki ranar Asabar

Shin daidai suke da kudaden intanet irinsu Bitcoin da Ethereum?

CBDC kai tsaye mallaki ne na Babban Banki kuma an samar da shi ne a hukumance. Hakan na nufin bankin koli zai iya amincewa ko soke ma'amala dashi tunda yana kula da abubuwan dake tafe tattare dashi sabanin sauran kudaden intanet.

Doka ce za ta amince da hulda da shi tare da cikakken iko.

Ya bambanta da sauran kudaden intanet masu zaman kansu. Doka bata amince da sauran kudade masu zaman kansu ba, kuma ba mallaki ne na wani Babban Banki ko wasu daga cikin cibiyoyin da aka kayyade ba.

Ba kamar nau'ikan sauran kudaden intanet ba da ke aiki ta hanyoyin sadarwa na blockchain ta hanyar da ba ta dace ba, CBDC mallakan kadari ne ta kasa da kuma kasar ke sarrafawa.

Ta yaya CBDC zai gudana?

CBN ya yi bayanin cewa tsarin eNaira CBDC ya hada da matakai 4 zuwa cikakken aiwatarwa da kuma tafiyarwa.

Read also

Da duminsa: Kotu ta dage shari'ar Nnamdi Kanu, jami'an DSS sun iza keyarsa

CBN ne ke da alhakin kerawa, kirkira da adana CBDC.

Za a rarraba CBDC ga cibiyoyin kudi da masu hada-hadar kudi masu lasisi wadanda za su ba da su ga mutane da sauran kasuwanni.

Cinikayya da CBDC na iya kasancewa akan yanar gizo ko akasin haka. Mutane da kamfanoni za su iya huldar kasuwa dashi nan take ta hanyar tashoshin biyan kudi na yanzu da na nan gaba (misali wayar hannu).

CBN za ta ci gaba da sa ido da kula da CBDC.

Gudummawar CBDC ga tattalin arzikin Najeriya

CBDC na iya rage farashin sarrafa tsabar kudi da 5%-7%, zai zurfafa hada-hadar kudi na intanet da habaka kasuwancin yanar gizo.

Zai inganta biyan kudade na kan iyaka cikin inganci, dacewa da araha.

CBDC zai kara zamanantar da tsabar kudi da habaka kasuwancin yanar gizo, gami da zurfafa hada-hadar kudi ta intanet.

Fa'idodin da zai iya samar wa ga gwamnati sun hada da samar da ingantacciyar hanyar da za a iya rarraba kudaden kasafi ga 'yan kasa.

Read also

Wakilin Birtaniya ya dira kotu domin shari'ar shugaban 'yan awaren IPOB

Babban bankin ya kara da cewa eNaira zai rage kaucewa biyan haraji da kwararar kudaden haram. Ana kuma sa ran kudin zai inganta cinikayyar kan iyaka, inganta hada-hadar kudi, inganta aikawa da kudi, da sauran su.

Source: Legit.ng

Online view pixel