Yadda aka sace wata budurwa bayan kammala digiri tana jiran shiga sansanin NYSC, kuma aka kashe ta a Makurdi

Yadda aka sace wata budurwa bayan kammala digiri tana jiran shiga sansanin NYSC, kuma aka kashe ta a Makurdi

  • Wata matashiya, Joy Onoh, ta rasa ranta bayan kammala karatun digirinta a ɓangaren jarida a jami'ar jihar Benuwai
  • Rahotanni sun bayyana cewa Joy tana siyar da kayan sawa, kuma ta rasa ranta ne a hannun wani da ya kira ta domin siyan kayanta
  • Rundunar yan sanda ta tabbatar da lamarin, tace bayan samun rahoton ne jami'ai suka gano gawar wacce ake nema

Benue - Wata budurwa yar kimanin shekara 24 wacce ta kammala karatun jarida a jami'ai jihar Benuwai, Joy Onoh, ta rasa ranta hannun wasu da ba'a gano su waye ba.

Dailytrust ta ruwaito cewa matashiyar ta rasa ranta ne a wani wuri da ake kira 'North Bank suburb' dake Makurdi, babban birnin jihar Benuwai.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu mutane sun sace Joy ne bayan sun bukaci ta kai musu abubuwan da take siyarwa.

Kara karanta wannan

Sai mun hada kai ne za mu iya cin galaba a kan miyagu – APC kan harin jirgin kasa

Joy Onoh
Yadda aka sace wata budurwa bayan kammala digiri tana jiran shiga sansanin NYSC, kuma aka kashe ta a Makurdi Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Tun bayan tafiyarta dai, wacce ta yi cikin gaggawa, Joy ba ta koma gida ga mahaifiyarta ba, kuma ana tsammanin sai da suka ci zarafinta kafin a kasheta.

An jefar da gawarta a a kan hanyar jerin gidajen gwamnatin tarayya dake North Bank a Makurdi.

Yadda lamarin ya faru?

Da take zantawa da manema labarai a Makurdi, mahaifiyar wacce aka kashe, Grace Onuh tace ɗiyarta ta kammala karatun digiri a watan Maris.

A cewar matar, wacce take zaune a bayan sakateriyar NUJ, marigayya ɗiyarta na jiran takardar kira na shiga sansanin bada horo na NYSC a rukunin C.

Punch ta rahoto Matar tace:

"Joy ba ta jimawa ba ta dawo gida ba, ina mata gyaran gashi lokacin da wani kwastoma ya kirata a waya ya bukaci ta kai masa kayan sawa irin wanda take siyarwa zuwa North Bank."

Kara karanta wannan

Da duminsa: Nnamdi Kanu ya bayyana a gaban kotu, an hana 'yan jarida shiga

"Cikin sauri ta kyale gyaran gashin da nake mata, ta ɗauki kayan da aka bukata ta nufi wurin. Na jira na jira bata dawo ba, na kirata a wayar salula ban same ta ba."
"Ta bar gida da misalin ƙarfe 5:00 na yamma amma da naga dare ya yi har ƙarfe 9:00 na dare, sai naje caji ofis na kai rahoto. Washe gari yan sanda suka gano gawarta."

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Da yake tabbatar da lamarin, kakakin rundunar yan sandan jihar Benuwai, DSP Catherine Anene, yace sun samu rahoton ɓatan matashiyar.

A cewarsa daga baya kuma jami'ai suka gano gawarta a wani jeji dake kusa da North Bank cikin Makurdi.

A wani labarin kuma Wani dan Saurayi ya hallaka dan okada kan N500 na siyan Data a wayar salula

Rahoto ya nuna cewa, Samson Odunayo, yana aikin damfarar mutane a yanar gizo, don haka yana bukatar Data.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan Bindiga Sanye Da Kayan Sojoji Sun Sace Matafiya 13 a Jihar Neja

Kwamishinan yan sandan jihar Ogun, Lanre Bankole, yace an kama masu laifin ne yayin da suka je siyar da mashin ɗin wanda suka sace.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel