Babbar Magana: Wani dan Saurayi ya hallaka dan okada kan N500 na siyan Data a wayar salula

Babbar Magana: Wani dan Saurayi ya hallaka dan okada kan N500 na siyan Data a wayar salula

  • Wani ɗan matashin saurayi ya kashe ɗan Okada kan N500 da yake nema ido rufe ya siya Data a wayarsa a jihar Ogun
  • Rahoto ya nuna cewa, Samson Odunayo, yana aikin damfarar mutane a yanar gizo, don haka yana bukatar Data
  • Kwamishinan yan sandan jihar Ogun, Lanre Bankole, yace an kama masu laifin ne yayin da suka je siyar da mashin ɗin

Ogun - Jami'an yan sanda sun damƙe wani ɗan saurayi, Samson Odunayo, tare da abokan aikinsa biyu, bisa zargin kashe wani ɗan okada da sace mashin ɗinsa a jihar Ogun.

Punch ta rahoto cewa Odunayo, ɗan shekara 18, ya amince da laifin da ake zarginsa, amma yace ya yi haka ne saboda yana bukatar N500 na siyan Data.

Read also

Babban dalilin da yasa yan Najeriya ba zasu amince da Igbo ya zama shugaban ƙasa a 2023 ba, Dokpesi

Odunayo, ya shiga hannun yan sanda ne tare da sauran abokan aikata ta'asarsa, Sodiq Awokoya da Jimoh Rilwan a yankin Ogere ranar Jumu'a.

Yan sanda
Babbar Magana: wani saurayi ya hallaka ɗan okada kan N500 Hoto: guardian.ng
Source: UGC

Da yake magana kan lamarin a hedkwatar yan sandan jihar, kwamishinan yan sanda, Lanre Bankole, yace jami'ai sun kama samarin ne yayin da suka yi kokarin siyar da mashin ɗin, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Shin kan N500 kacan suka kashe mutunin?

Da yake zantawa da manema labarai, Odunayo, wanda ya tabbatar da cewa shi ɗan damfara ne a Intanet, yace ya kashe mutumin ne saboda yana bukatar N500 ya saka Data.

A jawabinsa yace:

"Sadiq ne ya jawo ni zuwa aikata waɗannan ayyukan, kuma wannan shine aikin mu na biyu kafin a damƙe mu."
"Aikin farko da muka yi, ba mu kashe mutumin ba, mun karɓi kudi N3,500 ne daga hannunsa."

Read also

Yadda yan bindiga ke sako mutanen da suka kama ba tare da biyan kudin fansa ba a Zamfara

"Na biyu kuma na amince mu fita aikin ne saboda ina bukatar kuɗin Data, domin cigaba da harkata ta 'Yahoo Yahoo' amma ban taba kisa ba."

A wani labarin na daban kuma Kotu ta yanke wa wani bawan Allah da ya hallaka matarsa hukunci a jihar Kano

Wata babbar kotu a jihar Kano, ranar Talata, ta yankewa wani mutumi, Aminu Inuwa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Mutumin mai suna, Aminu Inuwa, ya musanta abinda ake zarginsa da shi, a cewarsa sam ba shine ya kashe matarsa ba.

Source: Legit

Online view pixel