Matar shugaban ƙasar Turkiyya ta kaddamar da muhimmin abu a Abuja yayin ziyarar mijinta

Matar shugaban ƙasar Turkiyya ta kaddamar da muhimmin abu a Abuja yayin ziyarar mijinta

  • Matar shugaban ƙasan Turkiyya, Emine Erdogan, ta kaddamar da cibiyar al'adun kasarta domin karfafa alaƙa da Najeriya
  • Emine tace musabbabin buɗe wannan cibiya shine domin kara karfin alaƙar al'adun Turkiyya da Najeriya da kuma koyon yaren Turkawa
  • Matar shugaban ta samu rakiyar matar mataimakin shugaban ƙasa da kuma ministan jin kai da walwala, Sadiya Farouk

Abuja - Matar shugaban ƙasar Turkiyya, Emine Erdoğan, ta kaddamar da cibiyar al'adun Turkawa a babban birnin tarayya Abuja, ranar Laraba.

Dailytrust ta rahoto cewa cibiyar, wadda aka raɗa wa suna 'Yunus Emre Institute' zata ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu.

Emine ta kaddamar da cibiyar ne bisa rakiyar matar mataimakin shugaban ƙasa, Mrs Dolapo Osinbajo, da ministan walwala da jin kai, Sadiya Umar Farouk.

Matar shugaban Turkiyya da Aisha Buhari
Matar shugaban ƙasar Turkiyya ta kaddamar da muhimmin abu a Abuja yayin ziyarar mijinta Hoto: @Aisha Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Meyasa ta buɗe cibiyar a Najeriya?

Emine ta bayyana cewa ta buɗe cibiyar ne a Najeriya sabida ƙara danƙon alaƙa tsakanin al'adun Turkiyya da Al'adun Najeriya.

Kara karanta wannan

Kada ku bar masu tsattsauran ra'ayin addini su kwace iko da Najeriya, Sarkin Musulmi ga Jami'an tsaro

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarta ta kaddamar da cibiyar ne domin wayar dakai kan al'adun Turkawa da kuma taimakawa wajen koyon yaren Turkawa.

Hakanan kuma cibiyar zata taimaka wajen musayar bayanai ta ɓangaren zane-zane, kimiyya, al'adu da kuma ilimin zamani, kamar yadda daily Nigerian ta ruwaito.

Alaƙar Najeriya ta Turkiyya

Dangane da alaƙar dake tsakanin ƙasashen biyu, Emine tace mutanen Turkiyya na yiwa nahiyar Africa kallon masu tasowa a ƙarni na 21.

Matar shugaban ta ƙara da cewa aƙalla ɗalibai 14,000 ne daga nahiyar Africa suka amfana da tallafin karatu na gwamnatin Turkiyya.

A wani labarin na daban kuma kun ji Babban dalilin da yasa yan Najeriya ba zasu amince da Igbo a matsayin shugaban ƙasa ba

Ɗaya daga cikin jiga-jigan PDP, Raymond Dokpesi, yace ba dalilin da zaisa yan Najeriya su amincewa ɗan Igbo ya shugabance su.

Kara karanta wannan

Jerin muhimman abubuwa 7 daga ganawar Buhari da shugaban kasar Turkiyya

Shugaban kamfanin DAAR yace kamata ya yi PDP ta sake baiwa Atiku Abubakar, daga yankin arewa maso gabas dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel