Kada ku bar masu tsattsauran ra'ayin addini su kwace iko da Najeriya, Sarkin Musulmi ga Jami'an tsaro

Kada ku bar masu tsattsauran ra'ayin addini su kwace iko da Najeriya, Sarkin Musulmi ga Jami'an tsaro

  • Mai alfarma sarkin Musulmi ya roki dakarun tsaron ƙasar nan da kada su bari jahilai su kwace ragamar mulkin ƙasa
  • Alhaji Sa'ad Abubakar, yace jahilai masu tsattsauran ra'ayin addini, suke jawo duk rikicin dake faruwa a faɗin Najeriya
  • Hafsan rundunar sojin ƙasa, Farouk Yahaya, yace ƙalubalen da Najeriya ke fama da shi yana bukatar taimakon kowa

Sokoto - Mai martaba sarkin musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar, ya yi kira ga hukumomin tsaron ƙasar nan su ɗauki mataki kan masu tsattsauran ra'ayi.

Yace irin waɗannan mutanen sune ke jawo duk wasu rikice-rikice ta hanyar gurguwan fahimta da suke wa koyarwan addini, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Basaraken ya yi wannan furucin ne a wurin taron ilimi na ƙasa na rundunar sojin ƙasa da ya gudana a jihar Sokoto.

Sarkin musulmai, Alhaji Sa'ad Abubakar
Kada ku bar masu tsattsauran ra'ayin addini su kwace iko da Najeriya, Sarkin Musulmi ga Jami'an tsaro Hoto: ripplesnigeria.com
Source: UGC

Sarkin yace:

Read also

Yadda yan bindiga ke sako mutanen da suka kama ba tare da biyan kudin fansa ba a Zamfara

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mutane da dama suna canza ma'anonin ayoyin littafi mai tsarki saboda ba su samu masu koyarwa nagari ba, musamman a manyan addinan nan biyu."
"Wannan babban ƙalubale ne, saboda haka, ilimi ne babban hanyar magance matsalar masu tsattsauran ra'ayi.
"Ya zama wajibi a kan mu kada mu bar irin waɗannan mutanen su kwace iko da wani ɓangare na Najeriya. Wajibi mu ƙalubalance su ta ilimi da kuma tsaro."

Shin gwamnati na ɗaukar irin wannan shawarin?

Sarkin musulmin ya kuma koka kan yadda ba'a amfani da abubuwan da aka cimma a taruka irin waɗan nan.

"Adadin yadda muka tattauna akan matasalolin mu, kamar haka zamu samu hanyoyin warware su, kuma da zaran mun aiwatar, ƙasar mu zata gyaru."

Ya kuma jaddada bukatar yan Najeriya su daina tunanin kwalin karatu, ta hanyar komawa tsarin samun ingantaccen ilimi, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Read also

An kuma, Miyagun yan bindiga sun kutsa fadar Basarake, sun yi awon gaba da shi a jihar Katsina

Ya kuma shawarci mahukunta cewa a rinka koyar da karatu a yaren al'umma a makarantu, inda ya ƙara da cewa hakan zai taimaka wa ɗalibai wajen fahimta cikin sauri.

Matsalar tsaro ta rataya wuyan kowa - COAS

Hafsan sojojin ƙasa, COAS Farouk Yahaya, yace ƙalubalen tsaro da Najeriya ke fama da shi yana bukatar haɗin kan kowa.

Ya roki baki ɗaya mahalarta taron da su taimaka da shawarwari masu ma'ana, domin rundunar soji ta ƙara zumma a kokarinta na kare rayuka da dukiyoyin yan Najeriya.

A wani labarin kuma Yan bindiga sun shiga uku yayin da Rukunin karshe na sabbin jiragen yaƙin 'Super Tucano' suka iso Najeriya

Ministan yaɗa labarai da Al'adu, Alhaji Lai Muhammed, yace sabbin jiragen 12 sun canza wasan, sojoji na cigaba da samun nasarori.

Ministan ya kuma yi martani kan rahoton cewa rundunar sojojin sama ta biya yan bindiga miliyan N20m don kada su harbo jirgin shugaban ƙasa.

Read also

Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun sake kai hari jami'ar Arewa, Sun yi awon gaba da dalibai

Source: Legit

Online view pixel