Jerin muhimman abubuwa 7 daga ganawar Buhari da shugaban kasar Turkiyya

Jerin muhimman abubuwa 7 daga ganawar Buhari da shugaban kasar Turkiyya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 20 ga watan Oktoba yayi wata ganawar sirri da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Shugaban na Turkiyya wanda ya isa da yammacin Talata, 19 ga watan Oktoba, yana Najeriya a ziyarar kwanaki biyu tare da uwargidansa Emine Erdogan.

An tattaro cewa shugabannin biyu sun yi magana a wani taron manema labarai na hadin gwiwa kan ziyarar aiki na shugaban na Turkiyya.

A cikin wannan rahoton, Legit.ng ta yi karin haske kan abubuwa bakwai da shugaban ya tattauna da takwaransa na Turkiyya.

Jerin muhimman abubuwa 7 daga ganawar Buhari da shugaban kasar Turkiyya
Shugaban kasar Turkiyya da shugaban Najeriya | Hoto: Buhari Sallau
Source: Facebook

1. Shugaba Buhari ya jinjinawa shugaban kasar Turkiya kan bude iyakokin kasarsa tare da karbar miliyoyin 'yan gudun hijira da ke matukar bukatar taimakon jin kai.

Read also

Sabbin kyawawan hotunan Shugaba Buhari da uwargidansa, Aisha sun bayyana

Shugaban na Najeriya ya bayyana cewa Erdogan ya ba da misali ga sauran kasashen duniya kan yadda ake mu'amala da 'yan gudun hijira.

2. Buhari ya bayyana ziyarar shugaba Erdogan da uwargidansa a matsayin wata alama ta "tsayayyen zumunci tsakanin 'yan Najeriya da Turkiyya."

3. Sun tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi kasashen biyu, da nufin karfafa dankon zumunci tsakanin kasashensu.

4. Cire Turkiyya daga jerin haramcin tafiye-tafiye na Najeriya dangane da sabbin ka'idojin Korona.

5. Shugaban na Turkiyya ya yi alkawarin cewa kasarsa za ta kara hada kai da Najeriya kan yaki da ta'addanci da kuma a fagen aikin soji, masana'antar tsaro da tsaro.

6. Shugaba Erdogan ya sanar da cewa, kasarsa ta kara yawan diflomasiyyarta a Afirka zuwa ayyuka 43.

7. Takwaran na Buhari ya jaddada cewa Turkiyya ta kuduri aniyar inganta alakarta da Najeriya zuwa ‘‘manyan matakai a dukkan fannoni ’’.

Shugaban Turkiyya ya gargadi Buhari, ya ce ya kula da masu shirin juyin mulki

Read also

Ganawar Buhari da shugaban Turkiyya: Abubuwa 5 da Najeriya za ta mora a ganawar

A bangaren ganawar, Shugaba Recep Tayyip Erdogan na kasar Turkiyya ya nuna damuwa cewa har yanzu kungiyar 'yan ta'adda ta Fetullah (FETO), wanda ya zarga da yunkurin masa mulkin ba a ranar 15 ga watan Yulin 2016, ya ce su ne a Najeriya.

Erdo spokean ya yi magana ne ranar Laraba a wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da Shugaba Muhammadu Buhari a yayin ziyarar aiki a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban ya gabatar da jawabinsa ne cikin yarensa na Turkiya wanda daya daga cikin jami'ai da ke tawagarsa ya fassara.

Source: Legit

Online view pixel