Mutane 15 Sun Mutu Yayin da Kwale-Kwale Ya Nutse da Su a Hanyar Zuwa Maulidi

Mutane 15 Sun Mutu Yayin da Kwale-Kwale Ya Nutse da Su a Hanyar Zuwa Maulidi

  • Akalla mutum 15 ne suka rasu yayin da wani Kwale-Kwale mai ɗauke da yan zuwa Maulidi ya kife a yankin karamar Shagari, jihar Sakkwato
  • Shugaban karamar hukumar, Aliyu Abubakar Dantani, yace mutane 25 Jirgin ya kwaso amma an tsamo 10 a raye
  • Mazauna yankin Shagari sun jima suna fama da lamarin haɗarin Kwale-Kwale tsawon shekaru

Sokoto - Aƙalla mazauna kauye 15 ne suka rasa rayukansu bayan Jirgin ruwan da suke ciki ya kife a hanyar ruwa a yankin ƙaramar hukumar Shagari, jihar Sakkwato.

Wakilin jaridar Daily Trust ya gano cewa lamarin ya auku ne yayin da mutanen ke hanyar zuwa ƙauyen dake makaftaka da su da nufin halartar taron Maulidi na murnar haihuwar Annabi Muhammad SAW.

Taswirar jihar Sakkwato.
Mutane 15 Sun Mutu Yayin da Kwale-Kwale Ya Nutse da Su a Hanyar Zuwa Maulidi Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Shugaban ƙaramar hukumar, Aliyu Abubakar Dantani, yayin tabbatar da faruwar haɗarin, yace mutanen da suka mutu sun fito ne daga ƙauyuka daban-daban.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike Ya Kara Kaɗa Hanjin PDP Kan Wanda Ya Dace Ya Gaji Buhari a 2023

Yace, "Mutane 25 ne a cikin Kwale-Kwalen lokacin da ya kife amma an samu nasarar tsamo mutum 10 a raye. Sun taho ne daga kauyuka daban-daban, suka haɗu a kauye ɗaya sannan suka hau Kwale-Kwalen."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Suna kan hanyar zuwa wani kauye ne domin halartar bikin Maulidi amma Kwale-Kwalen ya nutse kafin su isa garin. Mutum 15 suka nutse daga baya an tsamo gawarwakinsu kuma an musu Jana'iza."

A cewar Ɗangani, mutum hudu daga cikin 'yan kauyen Gidan Raket ne, uku daga Gidan Dawa, Bakwai daga Sabon Garin Sullubawa da kuma wata mace yar Tsohon Garin Sullubawa.

Game da alƙawarin gwamna Aminu Tambuwal a 2021 na samar da ƙunshin rayuwa a kauyen dake kewayen ƙaramar hukumar, Ɗantani yace, "Maganar na nan."

Yankin ƙaramar hukumar Shagari na fama da yawan haɗarin jirgaen ruwa na tsawon shekaru.

Kara karanta wannan

2023: Kura Ta Kara Turnuke Wa Atiku, Shugabannin PDP a Wata Jiha Sun Yi Fatali da Sunayen Tawagar Kamfe

Faatoci sun halarci wurin Maulidi

A wani labarin kuma Fastoci Da Rabaran Fiye Da 30 Sun Halarci Maulidin Annabi Tare Da Musulmi A Kaduna, Hotunansu Ya Kayatar

Fasto Yohanna Buru na cocin Christ Evangelical and Life Intervention Ministry Kaduna ya jagoranci fastoci da rabaran-rabaran zuwa wurin bikin Maulidi a Kaduna.

Fasto Buru, ya ce sun halarci Maulidin ne domin inganta hadin kai, zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin Musulmi da yan uwansu Kirista.

Asali: Legit.ng

Online view pixel