Dalla-dalla: Yadda ake gane masu kai wa 'yan bindiga bayanan sirri

Dalla-dalla: Yadda ake gane masu kai wa 'yan bindiga bayanan sirri

  • Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana hanyoyin gano ma su ba ‘yan bindiga bayanan sirri
  • A cewar sa idan ka ga mutum ya siya biredi sinki 20 zuwa 100, akwai alamar tambaya mai girma akan sa
  • Ya kara da cewa, idan ka ga mutum da wayoyi kamar 20 haka ya na neman yadda ze yi cajin su, ka sanar da jami’an tsaro

Kaduna - Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bai wa mazauna jihar Kaduna dabarun gano masu kai wa ‘yan bindiga bayanan sirri da taimaka mu su.

A cewar sa matsawar ka ga mutum ya na siyan sunkin biredi 20 zuwa 100, akwai alamar tambaya tattare da shi.

El-Rufai, yayin bayar da dabarun gano masu kai bayanan, ya ce duk wanda aka gani da alamar tambaya a yi gaggawar sanar da hukuma, Daily Trust ta ruwaito.

Read also

El-Rufai ya rubuta wasika, yana so a ayyana ‘Yan bindigan Arewa a matsayin ‘yan ta’adda

Dalla-dalla: Yadda ake gane masu kai wa 'yan bindiga bayanan sirri
Dalla-dalla: Yadda ake gane masu kai wa 'yan bindiga bayanan sirri. Hoto daga thecable.ng
Source: UGC
Kamar yadda ya ce: “Duk wanda ya zo siyan biredi sinki 20 zuwa 100, a siyar ma sa sannan a sanar da jami’an tsaro. Ko kuma idan ka ga mutum ya zo da wayoyi wurin 20 yana nema mu su caji, ka sanar da hukuma.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda Daily Trust ta wallafa, yayin ci gaba da yin bayani a kan masu taimaka wa ‘yan bindiga, rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce akwai alamar tambaya a kan wadanda su ke siyan man fetur a jarkoki ko galan kuma ya kamata makwabta su lura kwarai da wannan.

Jami’in hulda da jama’an rundunar na jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige ya ce: “Wasu daga cikin mutanen nan kwatsam za ka ga sun canja wurin kashe-kashen kudi.
"Ta yuwu ka ga mutum ya kara aure daga wata anguwar ko kuma ka ga mutum ya na waya wacce ta kansance abar zargi. Kuma haka nan za ka iya ganin zirga-zirgar mutum ta canja.”

Read also

Siyasar Kano: Ba inda zanje, Ina nan daram a jam'iyyar APC, Tsohon Gwamnan Kano ya maida Martani

Ya roki mutane musamman na kauye a kan su kula da hakan kuma su yi gaggawar kai korafi ga hukuma don bincike. Don haka ASP Jalige ya bukaci mutane su kasance ma su kula, kada su dinga sanar da mutane sirrin su.

“Mu na shawartar kada ka sanar da wani sai DPO, ba kowanne dan sanda ake fada wa irin wannan lamarin ba. Idan mutum ba ya so a gan shi a ofishin ‘yan sanda, zai iya kiran jami’in hulda da jama’an yankin su ta lambar waya don mu na sirrinta irin wannan labarin,” a cewar sa.

Kaduna: Sojin sama da na kasa sun ragargaji 'yan bindiga 50 a Birnin Gwari

A wani labari na daban, sama da 'yan bindiga 50 sojojin Najeriya suka ragargaza har lahira sakamakon luguden wuta ta sama da ta kasa a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Wannan nasarar da jami'an tsaron suka samu ta tabbata ne da kokarin dakarun sojin sama da na kasa a yankin Saulawa zuwa Farin Ruwa a karamar hukumar Birnin Gwari.

Read also

Rahoto: 'Yan bindiga sun sace sama da mutane 830 a jihar Kaduna cikin watanni 3

Kamar yadda gwamnatin jihar Kaduna ta samu labari daga rundunar hadin guiwar, jirgin yaki na sojojin sama ne suka samar da taimako ga dakarun sojin kasa da ke kusantar yankin Dogon Dawa zuwa Damari zuwa Saulawa.

Source: Legit

Online view pixel