Kaduna: Sojin sama da na kasa sun ragargaji 'yan bindiga 50 a Birnin Gwari

Kaduna: Sojin sama da na kasa sun ragargaji 'yan bindiga 50 a Birnin Gwari

  • Sama da 'yan bindiga 50 dakarun sojin sama da na kasan Najeriya suka sheke a Birnin Gwari, jihar Kaduna
  • Jirgin yaki ne suka fara sintiri tare da sheke 'yan ta'adda 5 a yankin Saulawa zuwa Farin Ruwa da ke Binrin Gwari
  • An sake hango wasu babura 50 a wurin Farin Ruwa, bayan sakar musu bama-bamai, sojin kasan sun bi ta kansu da harsasai

Birnin Gwari, Kaduna - Sama da 'yan bindiga 50 sojojin Najeriya suka ragargaza har lahira sakamakon luguden wuta ta sama da ta kasa a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Wannan nasarar da jami'an tsaron suka samu ta tabbata ne da kokarin dakarun sojin sama da na kasa a yankin Saulawa zuwa Farin Ruwa a karamar hukumar Birnin Gwari.

Kaduna: Sojin sama da na kasa sun ragargaji 'yan bindiga 50 a Birnin Gwari
Kaduna: Sojin sama da na kasa sun ragargaji 'yan bindiga 50 a Birnin Gwari. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Kamar yadda gwamnatin jihar Kaduna ta samu labari daga rundunar hadin guiwar, jirgin yaki na sojojin sama ne suka samar da taimako ga dakarun sojin kasa da ke kusantar yankin Dogon Dawa zuwa Damari zuwa Saulawa.

Kara karanta wannan

Kaduna: Jami'an tsaro sun halaka 'yan bindiga 10 a Giwa, sun ceci mutum 1

Bayan tsananta duba yankin, an hango 'yan bindigan a babura biyar, kusan kilomita hudu daga gabashin Saulawa. A take aka fara ragargazarsu kuma suka mutu.

Kamar yadda Samuel Aruwan ya wallafa a shafinsa na Facebook, bayan nan an hango kusan babura hamsin suna kokarin tserewa zuwa Farin Ruwa kuma cike da kwarewa aka far musu.

Ragowar 'yan bindigan da ba a halaka ba, dakarun sojin kasa sun bi ta kansu inda suka sheke su.

Jirgi mai saukar angulu na biyu ya sake kai dauki inda ya murkushe sauran 'yan bindigan da farmakin farko bai kashe ba.

Duba yanayin aikin da dakarun suka yi, ya fallasa cewa sama da 'yan bindiga hamsin farmakin hadin guiwar ya yi ajali.

Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana gamsuwarsa da irin aiki kuma ya taya dakarun sojin Najeriya murna kan nasarar nan. Ya yi kira gare su da su cigaba da tabbatar da mugun karshe ga 'yan bindigan.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun fafata da Boko Haram, an ragargaji 'yan Boko Haram da yawa

Kaduna: Jami'an tsaro sun halaka 'yan bindiga 10 a Giwa, sun ceci mutum 1

A wani labari na daban, 'yan bindiga goma da ke tafka barna a cikin jihar Kaduna sun hadu da ajalinsu bayan arangamarsu da jami'an tsaro, Aruwan ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Jami'an tsaron hadin guiwa sun tattaru inda suka yi arangama da 'yan ta'addan a Kwanan Bataru da ke wajen garin Fatika ta karamar hukumar Giwa kuma suka yi artabu.

"A yayin musayar wutan, goma daga cikin 'yan bindigan sun sheka lahira yayin da wasu suka tsere da raunikan harbin bindiga."

Asali: Legit.ng

Online view pixel