Sabbin kyawawan hotunan Shugaba Buhari da uwargidansa, Aisha sun bayyana

Sabbin kyawawan hotunan Shugaba Buhari da uwargidansa, Aisha sun bayyana

  • Sabbin kyawawan hotunan Shugaban kasa Muhammadu Buhari da uwargidansa, Hajiya Aisha sun bayyana
  • An gano shugaban kasar tare da mai dakinsa suna yi wa juna kallon kauna yayin da take gyara masa takunkumin fuska
  • Wadannan hotuna sun birge mutane da dama inda suka tofa albarkacin bakunansu

Wasu kayatattun hotuna na shugaban kasa Muhammadu Buhari da uwargidansa, Hajiya Aisha Buhari sun bayyana.

A cikin hotunan wadanda suka ja hankalin ‘yan Najeriya da dama, an gano shugaban kasar da mai dakinsa cikin wani yanayi da ba kasafai ake gani ba.

Kyawawan hotunan Shugaba Buhari da uwargidansa, Aisha sun bayyana
Kyawawan hotunan Shugaba Buhari da uwargidansa, Aisha sun bayyana Hoto: Bashir Ahmad
Source: Facebook

Uwargidan Shugaban kasar ta kasance tana gyara masa takunkuminsa na fuska yayin da suke yi wa juna kallon kauna dauke da murmushi a fuskokinsu.

Hadimin Shugaban kasa a shafukan sadarwa na zamani, Bashir Ahmad ne ya yada hotunan a shafinsa na Facebook.

Read also

Ganawar Buhari da shugaban Turkiyya: Abubuwa 5 da Najeriya za ta mora a ganawar

A saman hoton Bashir ya rubuta:

“Dan takaitaccen labari. Shugaban kasa da Uwargidan Shugaban kasa.”

Wadannan hotuna sun burge mutane da dama inda suka tofa albarkacin bakunansu

Legit.ng Hausa ta zakulo maku Wasu daga cikin martanin a kasa:

Muhammed Musa Kandi ya yi martani:

"Kyakkyawan iyali ."

Saminu Yusuf Abdullahi ya rubuta:

"Baba harda lumshe ido"

Aliyu Al Ameen Omar

"Baba na murmushi"

Buhari zai karba bakuncin shugaban kasar Turkiyya, Erdogan da matarsa

A gefe guda, mun kawo a baya cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai karba bakuncin shugaban kasa Recep Tayyip Erdogan na kasar Turkiyya na tsayin kwana biyu a ziyarar da ya kawo wa Najeriya daga Talata 19 ga watan Oktoba.

Wannan na kunshe ne a wata takarda da babban mataimakin shugaban kasa na musamman a fannin yada labarai, Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Talata.

Read also

Buhari zai karba bakuncin shugaban kasar Turkiyya, Erdogan da matarsa

Shugaban kasan ya samu rakiyar matarsa, Emine Erdogan, kuma zai shigo ta kasar Angola ne sannan ya karasa kasar Togo domin kammala ziyararsa.

Source: Legit

Online view pixel