Buhari zai karba bakuncin shugaban kasar Turkiyya, Erdogan da matarsa

Buhari zai karba bakuncin shugaban kasar Turkiyya, Erdogan da matarsa

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai karba bakuncin shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan
  • Shugabannin kasashen biyu za su duba wasu jerin yarjejeniya tare da sa hannu kan wasu takardun fahimtar juna
  • Erdogan zai kaddamar da cibiyar al'adun Turkiyya yayin da matarsa za ta kaddamar da wata makaranta duk a Abuja

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai karba bakuncin shugaban kasa Recep Tayyip Erdogan na kasar Turkiyya na tsayin kwana biyu a ziyarar da ya kawo wa Najeriya daga Talata 19 ga watan Oktoba.

Wannan na kunshe ne a wata takarda da babban mataimakin shugaban kasa na musamman a fannin yada labarai, Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Talata.

Shugaban kasan ya samu rakiyar matarsa, Emine Erdogan, kuma zai shigo ta kasar Angola ne sannan ya karasa kasar Togo domin kammala ziyararsa.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro raguwa yake yi ba karuwa ba, ku sauya labarinku: Buhari ya aika sako ga manema labarai

Buhari ya karba bakuncin shugaban kasar Turkiyya, Erdogan da matarsa
Buhari ya karba bakuncin shugaban kasar Turkiyya, Erdogan da matarsa. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC
"A yayin ziyarar, ana sa ran shugabannin kasashen biyu za su duba wasu jerin yarjejeniya da kuma sa hannu kan wasu takardu na fahimta.
"Har ila yau, shugaban kasa Erdogan da shugaba Buhari za su yi ganawar sirri kuma zai kaddamar da cibiyar al'adun Turkiyya a Abuja.
"Ita kuwa uwargidan Erdogan, za ta samu rakiyar Aisha Muhammadu Buhari inda za ta kaddamar da makarantar sakandare ta gwamnati da aka gyara a Wuse 11 a Abuja.
“Wata kungiyar tallafi ta kasar Turkiyya mai suna the Turkish Cooperation and Coordinating Agency, TIKA ce ta gyara makarantar," takardar tace.

Najeriya ta na kallon kasar Turkiyya a matsayin 'yar uwa, kuma ta na ganin wannan ziyarar a matsayin ginshikin karin dankon alakarsu.

Buhari ya yi magana da Shugaban Turkiyya game da muzgunuwar da Israila ta ke yi wa Falasdinawa

Kara karanta wannan

Da duminsa: FG ta mika sabbin korafi 7 kan Nnamdi Kanu a gaban kotu

A wani labari na daban, jaridar The Cable ta ce shugaban kasar Turkiyya ya kira Mai girma Muhammadu Buhari, ya na neman Najeriya ta taimaka wa kasar Falastina da goyon baya.

Majiyar ta ce Recep Erdogan ya fada wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari cewa ya na sa ran kasarsa ta nuna goyon bayanta ga mutanen kasar Falasdina.

Recep Erdogan ya yi wannan kira ne bayan hare-haren da kasar Israila ta kai wa Jerusalem da Gaza a lokacin da ya zanta da shugaban Najeriya a ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel